Aminu Alan Waka Yayi Martani Mai Zafi Akan “Fatal Arrogance”Wanda Harda Yakubu Muhammad na cikin Sa
Wani fim da ake shiryawa a kudancin najeriya wanda ake kira da “fatal arrogance” wanda ake yada akidar shi’a ne a cikinsa.
Wanda tuni yan shi’a a nigeria basu ji dadin wannan fim ba irin na yada akidar su, shine fitaccen mawaki aminu abubakar ladan wanda aka fi sani da alan waka yayi martani a shafinsa na sada zumunta a Instagram.
Ga abinda ya wallafa a shafin nasa.
“In ka ɗauke lalacewar Al’umar Musulmi da basu damu da baiwa addininsu kariya ba kamar yarda suke zagewa a wajen yakin akida. Wannan Fim da ake shiryawa ba ƙaramin barazana bane ga zaman lafiyar Al’uma a Nijeriya. Hakika muna da raunin wakilci a dukkan janibi na rayuwa.”
A cikin akwatin mayar da martani akan fustin ya kara da cewa
“bamu taba yaki da hukumar tace fim akan kundin tsarin mulki ba face akan hakkinmu da aka murɗa baya acikin dokar kasa baya acikin dokar Allah. muna masu rashin goyon bayan ƙaƙaba mana wani tarnaƙi da zai sa a ɗaure bakinmu a wajen faɗin gaskiya in mun ganta. wannan kam a haka nake har gobe. Babu wata hukuma a Nigeria da ta sanya yin wani rijista doke in ba a yi ba za a kaika kurkuku. irinsu CAC irin IRS da sauransu. kaɗai hukuncin shi ne idan akwai wani romo da ake bayarwa to ba za a baiwa wanda baiyi rijista ba. hakan ba zai hana in Aminu Ala ya karya dojar kasa ko ta jiha ba a gurfanar da shi a kotu a yi masa hujunci. kuma har gobe akan haka ake. Babu wanda ya isa ya hana sharia ko hukunci amma fa ka tilasta min yin rijista wannan babu hurumin ni na yi hakan sai da yarda ta kuma ban yarda ba. sannan in ni na yi wani abu da ya saɓawa musulunci sai ka kai ni kotu babu haufi akan haka. ka gane wannan.”
Wana magana haka take bamu da kishi addinimu