Kannywood

Sheikh Pantami Baba na ne, Jaruma Adaman Kamaye ta Dadin Kowa

Advertisment

Jaruma Zahra’u Saleh Pantami wacce aka fi sani da Adaman Kamaye a shiri mai dogon zango na Dadin Kowa wanda ake haskawa a tashar arewa 24 ta bayyana alakar da ke tsakaninta da ministan sadarwa, Sheikh Ali Isa Pantami a wata tattaunawa da jaridar Aminiya ta yi da ita.

Kamar yadda ta bayyana, ita ‘yar asalin jihar Gombe ce kuma ta yi karatun firamare da sakandare a Gombe.

Ta bayyana cewa duk wanda aka ji sunansa akwai Pantami dan gidansu ne kuma Sheikh Isa Ali Pantami kanin mahaifinta ne.

A cewarta ta shiga harkar fin ne ta uwar dakinta, Hajiya Zulai Bebeji saboda sun zauna tare a Saudiyya don haka bayan sun dawo ta bayyana mata burinta na shiga fim.w

Ta bayyana yadda ta hada ta daa Musa Mai Sana’a wanda ya sa ta a fim dinsa mai suna Hisabi daga nan ta shiga shirin fim din sosai bayan marigayi Sani SK da Alasan Kwalle sun zama mata tsayayyu biyu a industiri.

Ta bayyana yadda ta je tantancewar shiga shirin fim din Dadin Kowa na tashar Arewa 24 wanda tace sun fi mutane 70 amma ta ci nasarar zama zakakurar da aka zaba.

Ta bayyana alakar da ke tsakaninta da Kamaye inda tace mutunci ne kawai kuma yana mata gyara idan ya ga ta yi kuskure amma babu wata alakar soyayya a tsakaninsu.

Ta ce a shirye ta ke da tayi aure idan har ta samu mijin da take so kuma dayake lamarin aure sai mutum ya tantance ya kula da kyau.

Ta yi fashin baki dangane da hotunanta da suka bayyana a kafar sada zumunta tare da wani yaro inda tace ba aure su ka yi ba, hotuna su ka dauka na wani fim mai suna ‘Matar Yaro’.

Ta kuma bukaci masoyanta da su dinga fada mata gaskiya idan sun ga ta yi kuskure kuma a dinga yi wa ‘yan fim uzuri.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button