Kannywood

Fitattun Jaruman Kannywood 10 Da Suka Fi Yawan Mabiya A Instagram

Advertisment
Kafar sadarwa ta Instagram ta zama daya daga cikin manyan kafafe da taurari da jarumai ke tururuwar zuwa don kasancewa tare da masoyan su.
Jaruman naa amfani da bidiyo da hotuna wajen kayatar da masoyan su, hakan yake sanyawa a kullum suke kara samun karbuwa inda mabiya ke kwararowa suna nuna musu goyon baya.
A wannan karon zamu kawo muku jerin fitattun jaruman Kannywood guda goma da suka fi mabiya a kafar Instagram, inda suka hada da:

1. Rahama Sadau

Jaruman Kannywood

Jaruma Rahama Sadau ita ce ta zama ta daya a cikin jaruman Kannywood da suka fi yawan masoya a Instagram, inda take da yawan mabiya miliyan 2.5 a shafinta mai suna @rahamasadau.

2. Ali Nuhu

Instagram 3 1

Ali Nuhu yana da mabiya miliyan 2.3 a shafinsa na Instagram mai suna @realalinuhu. Fitaccen jarumin ya fito a fina-finai da yawa a masana’antar Kannywood hadda ma wadanda ba na Kannywood ba. Ali Nuhu ya samu damar kaiwa wannan matsayi ne sakamakon jajircewa da hakuri da yayi a masana’antar.
 

3. Hadiza Aliyu Gabon

Instagram 4

Hadiza Gabon da jarumi Ali Nuhu suna kunnen doki ne a shafin na Instagram, inda ita ma take da yawan masoya miliyan 2.3, abinda ya bambanta su kawai shine, Ali Nuhu ya fi Hadiza Gabon sanya hotuna da bidiyo a shafinsa, inda a yanzu haka Ali Nuhu yake da 14,294 Posts, ita kuma Gabon take da 164 Posts.

4. Maryam Booth/Hafsat Idris/Nafisat Abdullahi

A wannan karon jaruman Kannywood guda uku duka sunyi kunnen doki ne, inda duka suke da yawan mabiya miliyan 1.9 a shafukansu na Instagram, sai dai bambanci na yawan hotuna da bidiyo da suke wallafawa a shafukan nasu, inda @offficialmaryambooth, take da 4,490 posts, ita kuma a shafinta @official_hafsaidris20 ta na da 610 posts, sai kuma @nafeesat_official, wacce ke da 205 posts.
 

5. Fati Washa/Maryam Yahya/Aisha Humaira

Fatima Abdullahi wacce aka fi sani da Fati Washa, tana daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood wadanda ke cigaba da samun mabiya a kafar ta Instagram, Fati Washa, na da mabiya 1.6 a shafinta mai suna @washafati. Fati dai tayi suna ne a shekarar 2014 a lokacin da ta fito a cikin shirin fim din Hanyar Kano daa Hallaci a shekarar 2015.

 

Banda Fati Washa, sai ku Maryam Yahya, wacce ita ma fitacciyar jaruma ce da tauraruwar ta ke haskawa a masana’antar. Jarumar na da masoya miliyan 1.6 kamar dai Fati Washa. A yanzu haka dai jarumar na fama da rashin lafiya, hakan ya sanya ta shafe lokaci mai tsawo ba a ji duriyarta ba. Maryam ta sanya hotuna da biyo masu yawan 1,405 a shafinta mai suna @real_maryamyahaya.
Ita ma jaruma wacce tayi fice a cikin jaruman na Kannywood ta samu nasarar samun masoya miliyan 1.6, inda ta shiga cikin jerin jarumai na biyar da suka shigo cikin jerin.
 

6. Mansurah Isah

Instagram 12

Kowa dai ya san irin sunan da jaruma Mansurah Isah ta yi a duniya fim, a wannan karon jarumar ta shigo cikin jerin jaruman Kannywood da suka fi masoya a Instagram, inda ta zo a matsayin ta shida, Mansurah Isah na da masoya miliyann 1.5 a shafinta mai suna @mansurah_isah, inda ta wallafa bidiyo da hotuna 6,793.

7. Sadiq Sani Sadiq

Instagram 13

Jarumi na gaba shine Sadiq Sani Sadiq, wanda ya zo a matsayin na bakwai a cikin jerin fitattun jaruman Kannywood. Sadiq Sani Sadiq na da masoya miliyan 1.4, inda yake da post 1,183.

8. Ado Gwanja/Umar M Shareef

Ado Gwanja wanda ya yi suna sosai a fagen waka da kuma fina-finan barkwanci ya shigo cikin jerin jaruman na wannan shekarar, inda yake da masoya miliyan 1.3. Jarumi kuma mawaki Umar M Shareef yayi kunnen doki da Ado Gwanja inda shi ma yake da masoya miliyan 1.3.

9. Halima Atete

Instagram 16

Jaruma Halima Atete da ta yi fice wajen fitowa a matsayin mafadaciya a cikin fina-finanta, ta fito a matsayin ta tara a cikin jerin jaruman, inda take da mabiya miliyan 1.2 a shafinta mai suna @haleemaatete.

10. Yakubu Mohammed/Teema Makamashi

Na karshe a cikin jerin jaruman Kannywood sune Yakubu Mohammed da kuma Teema Makamashi, wadanda suka yi kunnen doki da mabiya miliyan 1.1 kowannen su, Yakubu Mohammed na amfani da sunan @yakubmohammed, sai kuma Teema Makamashi da take amfani da sunan @teema_makamashi.
A karshe akwai jarumai guda uku da yawan mabiyansu ya kai miliyan daya kowannen su, inda suka hada da jaruma Momi Gombe, Saratu Gidado da kuma Amal Umar, wadanda muke fatan za su shige cikin jerin manyan jaruman a shekara mai zuwa.
Sources :aysnovels

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button