Kannywood

Kafin na zama yar fim, na kanyi abun da….- Cewar Hauwa

Advertisment

Harkar fim wata harka ce da take canza rayuwar mutum ya zamo kamar ba shi ba, sabida yanayin rayuwar da ya ke samun Kansa a ciki, duk da ban san hakan ba, sai da na samu kaina a cikin ta, kuma duniya ta fara sanin fuska ta.
Jaruma Hauwa S Garba wacce aka fi sani da sunan Mama ce ta bayyana hakan, a lokacin tattaunawar su da wakilin jaridar Dimukaradiyya, a lokacin da take masa tambayoyi dangane da halin da su ke samun kan su, daga sun shiga harkar fim.
Ta ce “Gaskiya rayuwar taba bambanta sosai, sabida a da can da ba a sanni ba, kuma fuska ta ba ta bayyana kowa ya san ta ba, zan iya fita na yi harkokin rayuwa ta yadda na ke so babu wanda zai kula da ni, to amma a yanzu ba zai yiwu ba, saboda an san fuska ta, duk in da na je, don haka dole wasu abubuwan sai ka rage, don komai na ka a fili yake kowa ya sa maka ido” inji ta.

Hauwa S. Garba

 
Kazalika Hauwa S Garba ta kare maganar ta da cewar “Don haka mata da mu ke yi fim, ina rokon ku da ku kiyaye mutuncin ku, don kada a rinka kallon mu a matsayin matan da ba su da kamun kai” a cewar ta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button