Wata sabuwa! Irin matsalar Abduljabbar ta bulla a Yobe!
Wajibi ne al’ummar Jihar Yobe su tashi tsaye don ganin sun kare Jiharsu daga fitinar da take tinkararsu, irin fitinar da ta bayyana a Kano ta hanun Abduljabbar Kabara.
Wannar fitina fa tana da hatsarin gaske, don tana iya janyo bala’i kala daban-daban, na rashin albarka, da jefa Addinin al’umma cikin hatsari mai girma, tare kuma da mummunan rashin zaman lafiya.
Wannan mutumi mai suna Shareef al-Muhajir, ya nuna yana tare da Abduljabbar dari bisa dari, kuma har yake fitowa bainar jama’a yana sukar Hadisan Annabi (saw).
Kai, a gaskiya ta wani bangaren Shareef al-Muhajir zai iya fin Abduljabbar hatsari, saboda shi hatta Ayoyin Alkur’ani ba su tsira a wajensa ba.


Idan za a iya tunawa, a baya ya taba yin izgilanci da wasa da Ayoyin da suka zo suna magana a kan matan Aljanna (hurun ein). Don haka shi nasa gaba-gadin bai takaita a kan Hadisai ba, a’a, har ya isa kan Alkur’ani Mai girma.
Saboda haka muke ankarar da Malaman Jihar Yobe, su tashi tsaye su yaki wannar mummunar Akida kamar yadda Malaman Jihar Kano suka yi, ta yadda suka hada kai, suka nemi Gomnatin Jihar Kano ta taka ma abin birki.
Don haka muna fatan Al’ummar Jihar Yobe gaba daya – Gomnati da Malamai da Talakawa – za su tashi tsaye su yi abin da ya dace don ganin sun yaki wannar babbar fitina, don wanzuwar albarka da kare Addinin Mutane da kuma samun zaman lafiya a Jihar Yobe da Kasa baki daya.
Daga : malam Aliyu Muh’d sani









