Addini

Masha Allah: Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Ya Mayar Da Ginin Babban Cico “Kariye” Masallaci

Advertisment
Kariye gini ne daɗaɗɗe cikin ginin addini da tarihi shima ba zai manta da shi ba kamar ginin Hagia Sophia (Aya Sofiya), asalinsa coci ne, ya koma masallaci, ya koma gidan tarihi wajan ziyara, wanda yana cikin manyan waje goma da ake ziyara a kasar domin buɗe ido, wanda jiya juma’a ya ƙara komawa masallaci ƙarkashin umarnin Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, bayan kasancewarsa gidan tarihi tun bayan yaƙin duniya na biyu. 
Kariye gini ne na coci da aka gina a ƙarni na 6 a zamanin mulkin Byzantine, cikin Fatih a garin Constantinople (Istanbul) dake ƙasar Turkiyya, wanda har zuwa lokacin da Sultan Muhammad Al-Fateh, sarki daga daular Usmaniyya ya buɗe garin Constantinople (Istanbul), a shekara ta 1453, Kariye na nan a matsayin coci.
Kariye ya koma masallaci bayan bude garin Constantinople (Istanbul), da shekara wajan 58, a shekara ta 1511 ƙarkashin Sultan Bayazid II. Sai kuma ya koma gidan tarihi a watan Agusta na shekarar 1945, cikin sanarwa a shekara ta 1958, a gwamnatance daga majalisar ƙasar ta yi na ya koma gidan tarihi, da sunan cewa ƙasar bata addini ɗaya bace, kowa yana da haƙƙin yin addinin da yake so kamar yadda ya ga dama, bayan Kamal Atatürk ya tsotsa musu tsarin secularism na rusa musulunci da duk wata tutarsa da martabarsa, wanda a watan Nuwamba na shekarar 2019, majalisar ƙasar Turkiyya ta yi watsi da hukuncin mai da shi gidan tarihi.
Sai kuma jiya Juma’a, 21 ga watan Agusta na 2020, Kariye daga gidan tarihi wajan ziyara ya koma masallaci wajan ibadar musulmi, biyo bayan umarnin Shugaba Erdogan, wanda tuni aka miƙawa ma’aikatar addinin ƙasar Turkiyya masallacin na Kariye, domin buɗewa musulmi su fara ibada a ciki, idan ba a manta ba watan daya wuce na Yuli, aka mai da Hagia Sophia (Aya Sofiya) daga gidan tarihi zuwa masallaci shi ma kuma a ranar juma’a, 10 ga wata ƙarkashin umarnin Shugaba Erdogan, wanda yanzu haka ana sallah a cikinsa. 
Babu shakka Erdogan ya ƙara shiga kundin tarihi wajan raya addininsa, tarihinsa da kuma aikin mazan jiya na daular Usmaniyya da kuma ƙara shiga ran musulmi wajan ƙarfafa musulunci da yake, wannan abin alfahari gare mu, haka kuma ya ƙara jefawa maƙiyansa fargaba, tsoronsa da kwarjini wajan aiwatar da muradinsa. 
Tattara bayyani daga Jameel bn isma’eel

Paparoma yayi kuka tare da baƙin ciki da sauran ƙasashen kafirai da munafukai lokacin da aka buɗe Hagia Sophia (Aya Sofiya), yanzu bamu san yaya zai yi ba, yaya za su yi da baƙin ciki na ƙara buɗe Masallacin Kariye, tir! sai dai su mutu da baƙin ciki. 
Dawo da masallacin Kariye, busharar dawo da masallacin Qudus ne ga musulmi. Kamar yadda buɗe masallacin Hagia Sophia (Aya Sofiya) ga musulmi, busharar buɗe masallacin Qudus ne ga musulmi, tabbas rana za ta zo Qudus ya dawo hannun musulmi. 
Ina taya mutanen Turkiyya murnar dawo musu da masallacin Kariye, da sauran musulmin duniya baki ɗaya. 
Allah ya ƙarfafa musulunci da musulmi, ya ƙasƙantar da kafirci da kafirai, Aamiin. 
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button