Nomiss Gee Wakilin Shaidan A Doron Kasa – Indabawa Aliyu Imam
A yanzu haka za’a iya cewa al’ummar Arewa bata da babban kalubale a gabanta ta fuskar tarbiyya da addini sama da wannan shaidanin yaro da ake kira Nomis Gee.
Da ace mutanenmu na arewa sun san yadda wannan shaidanin yaro yake illata rayuwar yaransu ta hanyar lalata musu tunani ya hanasu karatu da abinda zai amfani rayuwarsu ya shigar dasu mummunar harkar nan mara amfani ta wake-wake irin na gayun kasashen turawan yamma wacce ke haddasawa matasa shaye-shaye da zinace-zinace da kazamar harkar nan ta neman maza wa’iyazubillah.
Da mutanen arewa sun san barnar da wannan yaro yake wa yaransu da tuni sun shiga sun fita sun dauki mataki a kansa, muna da masaniyya yadda wannan shaidanin yaro yake illata mana al’umma ta hanyar bin matasa har da ‘kananan yara yana kwadaita musu wannan mummunar harka yana shigo dasu ta hanyar haska su a shirin da yake yi gidan Tvn Arewa24, shirin da babu abinda ake nunawa sai badala da alfasha, ta yadda ake nuna mace musulma bahaushiya tayi mummunar shiga kanta babu dankwali ana ganin saman nonuwanta ga cikinta da cinyoyinta a bude, tana rawar banza ta Allah wadai, ka ga Namiji yayi tatoo yayi ass down shiga ta mashaya masu neman maza.
Tuni mun jima da gane gidan Tvn Arewa24 kwangilar yahudawa ce domin raba al’ummar arewa da addininsu, wallahi hatta wani ma’aikacin gidan ya tabbatar min da haka, kuma na kara gasgata hakan yadda ma’aikaciyar shirinsu na kwana casa’in tayi videon batsa, maimakon su dauki mataki a kanta ko su fito su nuna rashin jin dadinsu, sai ma suka ce hakan bai shafe su ba, ai ba’a cikin shirinsu tayi ba, suka cigaba da saka ta cikin shirin nasu na kwana casa’in, babu irin kokarin da Hukumar tace fina-finai ba tayi ba, amma saboda rashin samun goyon bayan gwamnati abun ya ci tura, idan har haka zai faru, ba zai zama abun mamaki ba, nan gaba idan Arewa24 ta fara haska abinda ke da alaqa da jima’i cikin shirye-shiryen da suke na hausa.
Muna baiwa iyaye shawara dasu kula da tarbiyyar yaransu, su kuma daina kunna musu munanan shirye-shiryen wannan tasha, kuma suyi amfani da wannan dama ta wannan wata mai albarka su kai karar wannan mutumi me suna Nomis Gee wajen Allah, har ma gidan arewa24 kamar yadda muke amfani da wannan dama mu yi addu’a akan bala’in Coronavirus.
Allah kaci gaba da tonawa Arewa24 asiri tare da sauran makiya addinin musulunci.
Indabawa Aliyu Imam

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)







