Yadda wasu Dalibai sunka kashe Abokinsu har lahira a Jihar Sokoto
Allahu Akbar majiyarmu ta samu wani wanda abun akwai ban takaici a ciki har da aminisa sunkayi sanadiyar kashe abokin karatunsu har lahira kamar yadda wani matashi ya bada labari Real Buroshi Mawaka Sokoto a shafinsa na sada zumunta inda yake cewa
Wasu ɗalibai sunyi sanadiyar mutuwar abokin karatun su a makarantar lafiya dake jihar Sokoto
Wasu ɗalibai a makarantar kiyon lafiya ta Sultan Abdurrahman School of health technology gwadabawa dake jihar sokoto, sun kashe abokin karatun su har lahira ta hanyar yimasa bugun akawo Wuƙa har yazamo sanadiyar mutuwarsa a daren jiya lahadi.
Ɗalibin maisuna Lukman wanda akafi sani da ( Khalifa) ɗan garin kalambaina mai karatu a sashen lafiyar haƙori ( Dental& surgery department) aji na biyu ( 200L) ya rasa ransa ne a sanadiyar wani zargin da abokan kwanansa keyi mishi wanda basuda tabbacin hakan, bayan Cece kucen da yafaru a tsakanin shi margayin da abokan nasa ne har yakai suka yimasa taron dangi suka zamo sanadiyar rasa rayuwarsa.
Wannan mummunan lamarin yafaru ne acen wajen makaranta cikin gidajen hayar kwanan su, ayanzu dai hukuma na kan ƙwakkwaran bincike gameda lamarin.
Allah ya Jikansa da Rahamarsa.”
Martanin mutane akwai wannan kisan dalibin.
@Rahilat Autah : ALLAH ya isar muna ka isar mai ka isarma musulunci akansu
Abin takaici hadda Amininsa wanda ko gida xaixo dashi yake xuwa wanda dan kaduna ne
Duk da cewar shi tuni ya tsere amma muna fatan hukuma ta kamoshi domin bimuna kadin jinin Khalifa wanda mukafi kira da Khalifan mama