Labarai
Bayan daurin aure, amarya ta gano cewa angonta bakanike ne ba dilan motoci ba
Advertisment
Wata budurwa ta bayyana yadda kawarta ta gano asalin sana’ar mijinta bayan an daura musu aure a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, musbizu.com.ng ta ruwaito.
Da alamu mutumin ya yi mata karyar cewa shi dilan motoci ne sai bayan an daura aure ta gano cewa ashe bakanike ne.

Kawar amaryar mai amfani da suna agneeess ta nemi shawarar jama’a akan abinda ya dace ayi tunda ba a kammala shagulgulan daurin auren ba. LH ta wallafa
Kamar yadda ta bayyana a Twitter:
“Kawata ta gano cewa angonta bakanike ne ba dilan motoci ba bayan an daura musu aure. Ya kuke ganin ya dace tayi?
“Abin lura anan shi ne ba a kammala liyafar auren ba..”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





