Da Gangan ‘Yan Fim Suke Janyo Abin Ce-Ce-Ku-Ce Don Hankali Ya Koma Kansu – Daso
A kwanan mabiyan jarumar a shafin Instagram suka kai miliyan daya, yayin da ba kasafai ake samun jarumai mata masu shekarunta da irin wannan adadi ba.
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa a Kannywood da ke arewacin Najeriya, Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso, ta ce wani lokacin da gangan ‘yan fim ke kirkirar wani abu da zai kai hankalin jama’a kansu.
Kamar yadda VOAHAUSA na ruwaito. Daso ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ta yi da Muryar Amurka.
“Kin san mu ‘yan fim kamar ‘yan siyasa muke, idan mun ga dama za mu rikita duniyar gaba daya ido ya dawo kanmu, wato idan mun ji rayuwar ta dan lafa muna so mu motsa ta.” Daso ta ce.
Jarumar wacce ta fi fitowa a matsayin mai barkwanci, ta bayyana hakan ne a lokacin da wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir ta yi mata tambaya kan wani bidiyo da ta wallafa a shafin Instagram inda aka ganta tana wanka a wurin waha (swimming pool)
“Da gangan na yi.” Daso ta kara da cewa.
“Sai da na kaikaici Lahadi babu kowa, na je na biya kudi, (na yi wanka) ni kadai sai kanwata da ta yi min bidiyo.” In ji jarumar wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu “Daham” da “Sansani” ta ce.
A kwanan mabiyan jarumar a shafin Instagram suka kai miliyan daya, yayin da ba kasafai ake samun jarumai mata masu shekarunta da irin wannan adadi ba.
“Alhadulillahi! Wannan mabiya miliyan daya da na samu a Instagram, baiwa ce daga Allah. Kafin na yi da yawa sun yi, wasu suna da fiye da miliyan daya.”
Ta kara da cewa, “abin da ya sa abin ya zama babba a idon jama’a, shi ne, saboda ganin ni dattijuwa ce kuma gani matar aure, shi ya sa ake cewa ya aka yi haka?
Fim na baya-bayan nan da jarumar take taka rawa a ciki shi ne, fim din “Gidan Danja,” wanda fim ne mai dogon zango.