Labarai
Kamfanin Coca Cola ya rage daraja har na dala biliyan hudu bayan Ronaldo ya kawar da kwalaben lemun a saman teburinsa yayin ganawa da manema labarai (bidiyo)


Advertisment
Kamfanin Coca Cola ya rage daraja har na dala biliyan hudu bayan Cristiano Ronaldo ya kawar da kwalaben lemun a saman teburinsa yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya maye gurbin su da robar ruwa.
Dama can Cristiano Ronaldo bashi da ra’ayi akan shan makamantan wa’yan lemukan saboda lafiyar sa, kuma a baya ya taba bayyana cewa baya son yana ganin yaron shi yana shan irin lemukan.
Kudin da Coka Cola ke samu ya rage daga dala 56.10 zuwa 55.22 bayan Ronaldo ya kawar da kwalaben nasu, wanda hakan yasa yanzu darajar kamfanin ta fado daga dala biliyan 242 zuwa dala biliyan 238.



