Kannywood

Ali Nuhu ya tsoma baki a diyyar da ake nema a hannun Hafsat Idris

Ali Nuhu ya tsoma baki a diyyar da ake nema a hannun Hafsat IdrisJarumi kuma mai bada umarni a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Ali Nuhu, ya shiga tsakanin jaruma Hafsat Idris da wani kamfani UK Entertaiment  har an samu sasanci, a babbar kotun jihar Kano, karkashin mai shari’a Zuwaira Yusuf.
Kamar yadda freedomradio ya ruwaito, Lauyan kamfanin ya bayyana a gaban kotun ranar a ranar Litinin 24-01-2022, domin ci gaba da shari’ar, sai dai ya shaida cewar, sun rufe karar biyo bayan sasanci da aka samu a tsakanin su da jarumar.
Tun abaya dai kamfanin, ya shigar da jarumar kara kan cewar, sun yi jarjejeniyar za ta yi masa wani aiki na TV Shoamw, a kan kudi Naira Miliyan Daya da Dubu Dari Uku, amma ta tsere, lamarin da ya sa su ka yi karar ta a gaban kotu.
Kamfain ya nemi ta biya su Naira Miliyan Goma a matsayin kudin damejin da ta yi musu, ta hannun lauyansu Ibrahim Abdulkadir Chedi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA