Labarai

Direban Keke-Napep ya dirka wa yarinya ciki a Kaduna

Matukin Adaidaita ya dirka wa yarinya ciki a Kaduna

A ranar Larabar nan ne wani dattijo mai suna Musa Sulaiman ya maka mai suna Umar Salisu da ke tuka babur din Adaidaita sahu a wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa, jihar Kaduna bisa zarginsa da yi wa diyar ciki.

Direban Keke-Napep ya dirka wa yarinya ciki a Kaduna
Direban Keke-Napep ya dirka wa yarinya ciki a Kaduna

Mai karan ya yi magana ta bakin lauyansu, Bar. Kabir Alhassan, ya ce Salisu ya yi alkawarin auren yarsa bayan faruwar lamarin amma ya kasa yin hakan bayan ta haihu.

Lauyan wanda ake kara Bar. I. H. Yahya, ya musanta zargin, inda ya ce wanda yake karewa ba shi ya yi wa yarinyar cikin ba kuma bai yi alkawarin aurenta ba.

Alkalin kotun, Abubakar Salisu-Tureta, ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Disamba domin masu kara su gabatar da shaidu.

Wani labari :Yadda Kotu Ta Daure Lebura Saboda Ya Saci Wake Kwano 7

Wata kotu ta yanke wa wani matashin lebura hukuncin daurin wata hudu a gidan yari kan satar kwano bakwai na wake.

Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa dubun matashin mai shekara 20 ta cika ne ne bayan ya balle shagon mai kara ya sace masa kwano bakwai na Wake da manja da kiret-kiret na lemo da sauran kayan abinci.

Ya kara shaida wa kotun da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, cewa sun gano baya ga kayan abincin, wanda ake zargin ya saci tukunyar gas da talabiji na bango da kudinsu ya kai N172,000

Laifin,a cewarsa ya saba wa sashi na 333, da na 336, da na 273 na kundin Penal Code.

Bayan sauraron karar, kotun ta yanke wa leburan hukunci, tare da ba shi zabin biyan tarar N30,000, da kuma karin wata N30,000 din ga wanda ya yi wa satar, ko ta kara masa wata guda kan daurin.

Alkalin ya ce ya yanke hukuncin ne domin ya zamo izina ga masu aikata laifuka irin haka.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button