Labarai

MATSALAR TSARO: Najeriya ta zama abin dariya a tsakanin kasashen duniya – TY Danjuma

Tsohon babban hafsan tsaron Najeria, Janar Theophilus Danjuma ya bayyana matsalar tsaron da ta addabi kasar a matsayin abin kunyar da ya sanya Najeriya zama abin dariya a tsakanin kasashen duniya.

Danjuma ya bukaci gwamnatin kasar da ta tashi tsaye wajen daukar matakan da suka dace na dawo da kimar Najeriya da kuma tabbatar da tsaron jama’a.

Janar Danjuma yace ‘yan kasashen waje ba za su yi sha’awar zuwa Najeriya ba domin zuba jari a cikin irin wannan yanayin da kasar ta samu kanta na rashin tsaro.

Tsohon ministan tsaron yace a halin da ake ciki yau, kasashen duniya na yiwa Najeriya dariya saboda gazawar da ta yi wajen samar da tsaro ga jama’ar ta.

Ko a ranar talatar da ta gabata, sanda kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Global Rights’ ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadarin rayuwa saboda yadda ‘yan bindiga ke cin karen su babu babbaka wajen kisa da garkuwa da mutane da kuma cin zarafin jama’a.

Bayan mayakan boko haram, ‘yan bindigar dake aika aika a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun zama wata masifar da ta hana kwanciyar hankali a jihohin dake yankin.

Rfihausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button