Kannywood

Allah yayiwa Jarumar Kannywood, Khadija Abubakar Mahmud Rasuwa

ALLAHU Akbar! Masu iya magana su ka ce rai baƙon duniya. Wannan batu haka ya ke.
A safiyar yau Alhamis, 6 ga Mayu, 2021 Allah ya yi wa jaruma Khadija Abubakar Mahmud rasuwa.
Khadija ta rasu a garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, da misalin ƙarfe 6 na safe a hannun mahaifiyar ta a kan hanyar su na zuwa asibiti.
Cikin alhini, mahaifiyar ta shaida wa mujallar Fim cewa sun ɗauki Khadija sun kai ta wani asibitin kuɗi, amma da zuwan su likitocin asibitin su ka ga halin da ta ke ciki sai su ka tura su Federal Medical Centre.
A kan hanyar su ta zuwa asibitin da aka tura su ne Allah ya ɗauki ran jarumar.

Award din margayi kenan

Marigayiyar ta rasu ta na da shekara 35 a duniya.
Khadija ta ɗauki tsawon shekara ɗaya ta na gama da rashin lafiya. Ta yi fama da wani irin ciwo ne wanda ke ƙone jinin jikin ta wanda ke sawa jini ko leda nawa aka saka mata lokaci kaɗan zai ƙone.
A haka dai ta samu lafiya na wasu lokuta, sannan kuma ciwon ya dawo.
Allah ya jiƙan ta da rahama, ya sa ƙarshen wahalar kenan, amin.
Kaɗan daga cikin finafinan da ta fito a ciki sun haɗa da ‘Rikicin Duniya’, ‘Uwar Miji Ko Kishiya’, da kuma ‘Uwar Miji Na’.
Majiyarmu ta samu labarin daga shafin fimmagazine.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button