Kannywood
Aminu Ala: Mawakin ya ce Hukumar fina-finan Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙi
Fitaccen mawakin Hausa, Aminu Abubakar, wanda aka fi sani da Aminu Ala ya ce hukumar tace fina-finan jihar Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙin yabon Annabi.
Aminu Ala ya shaida wa BBC Hausa cewa yin hakan daidai yake da “matse tunanin” mawaƙa saboda “ba a tace fasaha”.
A kwanakin baya ne, hukumar tace fina-fanai ta Kano ta ce babu wani sha’iri da zai ƙara fitar da waƙa a jihar, sai ta ba shi lasisi.
Shugaban hukumar Isma’il Muhammad Na’abba wanda aka fi sani da Afakallah ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.




