Labarai
Fadar Sarkin Kano Ta Fitar Da Sanarwa Gobe Litinin Za’a yi Jana’izar Mai Babban Ɗaki
Advertisment
Fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ta ce, za a yi jana’izar marigayiya Mai Babban Ɗaki a gobe Litinin 26 ga watan Afrilun da muke ciki.
Wannan na cikin wata sanarwa da Madakin Kano Alhaji Yusuf Ibrahim Chigari ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce, ana tsammanin isowar mamaciyar filin jirgin saman Malam Aminu Kano a yau Lahadi bayan sallar magariba.
Sanarwar ta kuma ce, za a kai mamaciyar hubbaren Gidan Sarkin Kano.
Muna addu’ar Allah ya gafarta mata, ya yi mata rahama tare da magabatan mu, da dukkan musulmai.




![[Bidiyo] yadda wani magidanci yayiwa fuskantar matarsa dameji bayan ya kamata tana hira da abokinta na Facebook](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/01/duka.jpg?resize=390%2C220&ssl=1)


