Labarai

Zaben 2023 tarihi ka iya maimaita Kansas, a shekarar 1979 anyi irin wannan haduwar tsakanin bangaren kudu maso gabas, kudu maso yamma da Kuma arewacin Nigeria

Awancan lokacin arewa ta tsaida mutum biyune Kuma dukkansu daga arewa maso yammaci suka fito watau SHEHU SHAGARI daga sokoto Sai Kuma MALAM AMINU KANO daga kano.

ZIK daga kudu maso gabas saikuma AWOLOWO daga kudu maso yamma, Bisa ga hasashena yanzunma hakan zata kaya banbancin kawai shine yan takarkarin na arewa daya ya fitone daga arewa maso gabas da Kuma daya daga arewa maso yamma.wani marubuci kuma mai bincike Mustapha sarkin kaya ya wallafa a shafinsa.

Awancan lokacin Malan aminu kano Bai Hana shehu shagar zama shugaban Nigeria ba dukda nasarar da ya samu na ragewa SHAGARI kuriun kano da Dan Wani bangare na arewa,

SHAGARI ya canye arewa da Wani bangare na kudu maso kudu harda Huda Wani banagaren kasar yarbawa.

AWOLOWO ya canye kasar yarbawa haka Shima ZIK ya canye kasar Igbo Amma duk wannan Bai Hana SHEHU SHAGARI zama shugababa.

Tabbas za a sake kwatawa atiku zai fadi kano Amma dukda hakan zaija kuriun kanawa zai Kuma kusan kwashe kuriun arewa ta tsakkiya da arewa maso gabas zaici sokoto,kebbi,zamfara haka zai kusan kwashe kuriun kudu maso kudu watau Niger delta.

KWANKWASO zaici kano da Wani kuriun daga Katsina zamfara da kaduna.

BOLA TININBU Zai zarra a kasar yarbawa Kuma zaija kuriun arewa maso yamma sosai haka PETER OBI zai gaji ZIK zai canye kasar Igbo saboda haka ATIKU zai kafa gwamnati da Dan karamin rinjaye.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button