Labarai
Gobara ta yi sanadiyar mutuwar majinyata 80 a asibitin masu fama da cutar corona
Akalla mutane 80 ne suka rasa rayuansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi a wani asibitin masu fama da cutar covid-19 a kasar Iraki.
Kamar yadda FREEDOMRADIO na ruwaito, rahotanni sun ce da dama daga cikin wadanda suka mutun suna karbar magani ne a asibitin na Ibn al-Khatib da ke gabashin birin Bagadaza
Jama’ar kasar dai sun yi ta allawadai da hukumomin kasar wadanda suka zarge su da sakaci lamarin da ya sanya firamoinistan kasar ta Iraki Mustafa al-Kadhemi ya dakatar da ministan lafiyar kasar Hassan al-Tamimi, wanda yak e samun goyon bayan fitaccen malamin Shi’ar nan Moqtada Al-Sadr