Labarai

Dana auri wanda bashi ganin darajar kwankwaso gwanda na zauna Babu aure har abada ~ Inji wata Budurwa

Wata budurwa a jihar Kano taki amincewa da bukatar auren wani saboda Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Jagoran Darikar Kwankwasiyya.
Budurwar mai suna, Lubna Ali, ta shaidawa jaridar Mikiya cewa, baza ta taba auren mutumin da ke nuna rashin ladabi ga jagoranta na siyasa Kwankwaso ba ko da kuwa za ta zauna ba ta da Aure.
“Na ki amincewa da bukatar Aure Saboda mai girma Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, duk da cewa bai sanni ba. Amma ina matukar kaunarsa”, inji ta.
A cewar Lubna, ‘Kwankwaso ya wuce matsayin dan siyasa, ina kallonsa a matsayin Shugaba, Uba kuma Jagora”.
Lubna ta ce, ta fara bin ra’ayin Akidar Kwankwaso ne tun tana ajin Karamar Sakandire a shekarar 2003.
“A lokacin ban san mene siyasa ba amma sunan Kwankwaso yana kaina.
“Zan iya tunawa motata ta farko Ja ce da hoton Kwankwaso gabadaya a jiki”, Inji ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button