Labarai

Duk Da Dangote ya ci amanar soyayyar da muka murza sau dubu-dubu, na amfana da shi – Budurwar Dangote ‘yar Amurka

Advertisment

Wata tsaleliyar mata ‘yar kasar Amurka mai suna Bea Lewis ta tona wani soyayya da ta yi da Hamshakin Attajiri, Aliko Dangote a Kasar Amurka, wanda ta ce ya ce amanar ta da soyayyar da ke tsakanin su sau dubu-dubu.
Kamar yadda PREMIUM TIMES Bea Lewis ta saka hotunan ta da Dangote rungume da juna, sannan ta rubuta cewa Dangote ya rika wulakantata akai akai fiye da sau dudu-dubu, sai dai kuma ta amfana da shi matuka domin a zamanta da shi ta fahimci harkar kasuwanci, tattali da tsananta yin hakuri.
” Hira kawai da na rika yi da attajiri irin Dangote, fitacce a duniya yakan kwantar min da hankali. Sannan kuma na koyi abubuwa da dama a rayuwa, kuma na samu daukaka da arziki masu yawa.
Lewis ta kara da cewa a dalilin Dangote, ta daina aikin saida tuwo-tuwo, ta fada harkar siyan hannayen jari, sannan kuma ta mallaki gidaje biyu nata, kuma ta dilmiya cikin harkar kasuwanci gadangadan.
” Wani abu da na koya a zama na da Dangote shine yadda ya rika tausa ni yana min khuduba da in rika hakuri a cikin al’amurorina, in rika kama kai na da kuma yin tawali’u a koda yaushe.
A karshe, PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin kakakin rukunin Kamfanonin Dangote ko sun san da wannan magana amma hakan bai yiwu ba, basu amsa waya ba.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button