Labarai

Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II: Tabbas Kare Zai Mutu Da Haushin Kura, Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Ya ku ‘yan uwa masu daraja, kamar yadda kuka sani ne, a satin da ya wuce, lokacin da ‘yan uwan mu Musulmi, karkashin Darikar Tijjaniyyah, suka gudanar da taron maulidin Shehu Ibrahim Nyass, wanda suka saba gudanarwa a kowace shekara; a wurin wannan maulidi ne aka gabatar da wani mashahurin majalisi, inda Sheikh Makkiy Nyass ya gabatar da wani muhimmin jawabi, wanda yake kara tabbatarwa da duniya game da jagoranci da matsayi da kuma Khalifancin Sarki Muhammadu Sanusi II a cikin Darikar Tijjaniyyah a Najeriya da ma duniya baki daya. Bidiyon wannan sanarwa ta Sheikh Makkiy Nyass ya yadu sosai, mun tura maku shi, duk kun gani, kuma kun shaida.
Bayan ayyana wannan sanarwa, kwatsam, sai hankalin makiya ya tashi, suka rude, suka rikice, suka dimauce. Suka kasa zaune, suka kasa tsaye, suka kasa bacci, kuma suka fara tunanin cewa to yanzu wace irin karya zasu kirkiro, ko kuma wane irin sharri ko makirci ko kazafi zasu kullawa Sarki Muhammadu Sanusi II, wai domin su kunyata shi a idon duniya.
Wallahi, ‘yan uwa, Allah ya sani, ban so yin magana akan wannan sha’ani ba, kasancewar ni ina sane da cewa Sarki Muhammadu Sanusi II baya da matsala da kowa; baya da matsala da ‘yan Tijjaniyyah, baya da matsala da ‘yan Izalah, baya da matsala da ‘yan Salafiyyah, kai ba ma Musulmai ba, wallahi hatta kiristoci, wadanda suka tsaya akan gaskiya, da son zama lafiya, Sarki Muhammadu Sanusi II baya da matsala da su, domin shi yana zaune ne da kowa lafiya, tare da fahimtar juna, da kuma mutunta juna.
Abun da ya jawo har zan yi magana akan wannan al’amari shine, mu a wurin mu, wannan al’amari ba wani babban al’amari bane da har zamu yi ta hayaniya ko bata lokacin mu akan sa. Kawai mu mun dauke shi wani karamin al’amari, domin muna da yakini akan irin girma da matsayi da Allah yayi wa Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II.
Ana cikin haka kwatsam, sai muka ga cewa, ashe su makaryata, magauta, makiya, makirai, maha’inta masu hassada da ikon Allah, sun dauki wannan abun wani babban al’amari, wanda daga karshe har yasa suka fara rubutu akan sa, tare da yada karya da shubuha, domin su rikitar da al’ummah, su rikitar da bayin Allah, su jefa rudani da rura wutar gaba da hassada da kiyayya tsakanin bayin Allah, kamar yadda suka saba yi a koda yaushe. To shine ni kuma naga wajabcin yin wannan rubutu, domin bayyanawa al’ummah gaskiya, tare da warware shubuhar wannan jahili Abba Anwar da mai gidansa Gwamna Abdullahi Ganduje, da ire-iren su. Domin duk lokacin da mabarnaci yayi barnarsa, to kuskure ne mutane suyi shiru, su ki bayyanawa duniya gaskiyar lamari. Domin ta nan ne shedan la’ananne yake rudar wasu bayin Allah na kwarai, sai a wayi gari sun rudu da shacifadin masu yada barna a bayan kasa da sunan gyara!
Mu kuwa wallahi aikin mu ne, ko zaka harbe mu, ko zaka yi gunduwa-gunduwa da mu, sai mun bayyanawa duniya gaskiya da yardar Allah! Ba ma tsoron kowa sai Allah Mahaliccinmu. Munyi imani dari-bisa-dari cewa rayuwar mu, da mutuwar mu; abincin mu da arzikin mu duk suna hannun Allah ne Madaukaki!!
Ya ku jama’ah, wani makaryaci, wai shi Sakataren yada labaran Gwamnan Jihar Kano, mai suna Abba Anwar, yayi wani rubutu shekaran jiya alhamis, 18/03/2021, mai taken: “Halifancin Tijjaniyya: Jagoran Dariqar Tijjaniyya Na Duniya Sheikh Mahy Sheikh Nyass Ya Ce Ba Su Aiko Da Kowa Ga Kowa Ba.” Wannan mutum ya sharara karyarsa da suka saba yi iya son ran sa, yadda yake so, a cikin wannan rubutu na shirme da bata lokaci, domin ya kau da hankalin wawaye da bayin Allah nagari, amma sai dai Allah bai bashi sa’a ba, Allah ya tozarta mugun nufin su, domin wallahi al’ummah sun san karya yake yi, sun san cewa karya kawai ya rubuta a cikin wannan rubutu nasa, don haka sai wannan rubutu bai samu karbuwa a wurin kowa ba, kuma Allah ya kunyata shi shi da mai gidansa Ganduje da yake yiwa aikin yiwa bayin Allah sharri da kazafi da karya.
Ya ku ‘yan uwa, wallahi, ni tun da nike jin tarihin kiyayya da makiya, tun da nike jin tarihin hassada da mahassada, ban taba ji ko ganin kiyayya a wannan karni ba irin wadda Ganduje da jama’arsa suke yiwa Khalifah Sarki Muhammadu Sunusi II.
Amma alhamdulillah, da yardar Allah babu komai, khairan In Shaa Allah. Har kullun Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II shine a samansu da ikon mai duka!
Ya ku jama’ah, kamar yadda kuka sani ne, wallahi Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II bai nemi wannan mukami ba, kuma bai taba neman a bashi ba, bai taba yiwa kowa magana akan nuna sha’awarsa ba, a’a, shi Sheikh Makkiy Nyass ne ya duba, yaga cancantarsa da dacewarsa, shine ya furta matsayinsa da na ‘yan uwansa akan sha’awarsu ta kara jaddadawa Sarki Muhammadu Sanusi II wannan matsayi na jagoranci da Khalifancin Darikar Tijjaniyyah.
Saboda haka anan abunda nike so ‘yan uwa su gane shine, su wadannan makirai, masu adawa da ikon Allah, sun manta da cewa, shi Sarki Muhammadu Sanusi II, mutum ne da Allah yayi wa daukaka, don haka, da a bai wa Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II wannan matsayi da kada a ba shi, yana nan dai tare da darajarsa da Martabarsa da kuma Muhibbarsa. Kuma abunda yake bayyane a fili shine, su wadanda suke bayar da wannan matsayi, ai sun riga sun bayar da izinin Allah.
Kuma duk wannan adawa da suke yi da ikon Allah, idan mun lura, da ma ai tarihi ne yake ta maimaita kan sa ayau. Irin abunda ya taba faruwa kenan a lokacin da aka cire Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi I, daga baya Shehu ya ayyana shi a matsayin Khalifan Tijjaniyyah, ai sai wasu suka fara adawa da lamarin, sanadiyyar haka sai Darikar Tijjaniyyah ta shiga rudani da rarrabuwar kai. Wanda idan baku manta ba, ai abun da kawai ya daidaita Darikar Tijjaniyyah a lokacin, kuma aka samu zaman lafiya da hadin kai, shine ba wa Sarki Sanusi I murabus Khalifancin Tijjaniyyah. Sai yayi amfani da iliminsa da basirar sa ya kawo zaman lafiya da ci gaba a cikin Darikar. Don haka ya kamata duk wani Dan Darikar Tijjaniyyah da Shehunnansu su san wannan, don haka bai kamata suyi wasa da tarihi ba.
Domin wannan ne nike kiran jama’ah cewa, wallahi kada mu yarda wasu shedanun mutane, da wasu shashashun ‘yan siyasa, wadanda ba su san ciwon kan su ba, basu san ciwon al’ummar su ba, suyi amfani da hankulan mu, su kawo muna rudani da hayaniya da rarrabuwar kai. Musamman ma ‘yan uwana ‘yan Darikar Tijjaniyyah, ya kamata su sani, kar su yarda shedanun ‘yan siyasa su rikita masu al’amari, kar su yarda shedanun ‘yan siyasa su raba kawunansu kamar yadda suka raba kan zuri’ar gidan Dabo, suka jefa kiyayya da gaba a tsakaninsu, ta hanyar yin amfani da lalatattun cikinsu, suka tozarta gumi da wahalar magabatansu!
Sannan kuma shi Sheikh Makkiy Nyass daya fadi wannan maganar a wurin majalisi, ai ya fade ta ne akan abunda ya sani a zukatan sauran Shehunnan da suka rage da Khalifofin Shehu Ibrahim Nyass. Don haka wadannan makiya, ‘yan siyasa, su sani, wallahi ko sun ki, ko sun so Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II ya zama Sarki, kuma dole ne a kira shi Sarki har abada, babu wanda ya isa ya hana hakan. Sannan Muhammadu Sanusi II darajarsa da Martabarsa kullum karuwa suke yi fiye da yadda darajarsa take yana gidan Dabo. Sannan Muhammadu Sanusi II tsayayyen mutum ne da aka yi masa shaidar son ‘yan uwansa tsakani da Allah, tare da son hadin kai na zumunci har kawo yanzu. Koda yake wallahi duk abinda zan fada sun fi ni sani, amma butulci da hassada basu bari su mika wuya ga bin gaskiya.
Kai jama’ah, ina ma ace wadannan mutane, wadanda Allah ya halitta da rayuwar butulci, sun yarda da zabin da Allah yayi, ba tare da sun sanya kiyayya da hassada a zukatansu ba! Gashi dai kun raba zumunci, kuma Allah da Manzonsa (SAW) sun tsinewa duk wanda yayi sanadiyyar raba zumunta; kun haddasa gaba da kiyayya tsakanin zuri’a daya, daga karshe kuma kun kare cikin rashin daraja da kamala, sai kuka zama tamkar mujiya a cikin al’ummah. Babu mai son ku, babu mai girmama ku, babu mai ganin mutuncin ku da girman ku sai ‘yan siyasar da suka dora ku kuyi masu aiki. Kai, Allah wadaran naka ya lalace…
Ya ku jama’ah, ku sani, Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II tun fin azal shi Khalifah ne, kasancewar sa Musulmi mai imani. Domin Allah ne da kansa ya tabbatar da Khalifancin mutum a bayan kasa, a cikin Alkur’ani, Suratul Bakarah, aya ta 30. Allah ne da kansa yace zai sanya Dan Adam ya zama Khalifah a bayan kasa. Kenan da wannan, Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II Khalifah ne. Sannan abu na biyu shine, duk duniya ta shaida cewa, tun farkon hawan Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II akan Sarautar Kano, a lokacin da take Sarauta, kafin Ganduje ya lalata ta, ya bata ta, ya tozarta ta, ya mayar da ita wani bangare na jam’iyyar siyasar su, Khalifah Sheikh Ahmadu Tijjani Nyass ya aikowa da Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II da Ijazah tare da takardar tabbatar da matsayinsa a cikin Darikar Tijjaniyyah. Shi kuma Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayar da amsar wannan takarda a rubuce, tare da bayyana godiyarsa ga Allah, na dora masa wannan matsayi, kuma a ciki ya bayyana karbar wannan matsayi, tare da rokon Allah yayi masa jagora.
Wadannan takardu guda biyu, mun yada su kwarai, duniya ta gan su, kuma ta shaida akan haka, domin mu bamu yin komai sai da hujja da kuma dalili.
‘Yan uwa na takardu ne guda biyu: ta farko Ijazah ce daga Senegal, wadda Khalifah Sheikh Ahmadu Tijjani Nyass ya aikowa da Mai Martaba Sarki lokacin da ya zama Sarki. Ta biyu kuma amsar da Sarki ya bayar ce akan wasikar. Kuma ita ce takarda ta farko a matsayin amsa, da Mai Martaba ya fara rubutawa a lokacin da ya zama Sarki.
Kuma ai da ace mutane basu manta tarihi, da bai kamata ace mun manta da cewa hayaniya irin wannan, wata dabi’a ce da Khalifanci ya gada tun fil azal, don haka ba wani sabon abu bane da aka fara kan Sarki Muhammadu Sanusi II ba. Dama mu ai muna sane cewa sai makiya sun yi haka.
A lokacin Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi I murabus ma ai yasha fama da irin wadannan matsaloli daga wasu malamai da makiya a Kano da wajen Kano, lokacin da ya zama Khalifah. Sannan shi ma Khalifah Sheikh isiyaka Rabi’u, Khadimul Islam, kuma Khadimul-Kur’an na gaskiya, ba na cuwa-cuwa ba, shima ai anyi irin wannan hayaniya da aka bashi wannan matsayi. Don haka babu wani sabon abu anan, abu ne da yake dabi’a a cikin irin wannan al’amari.
Kuma da man ai mu mun sani, domin irin yadda Allah ya haskaka Mai Martaba Sarki a taron maulidin nan na Sakkwato, aka wayi gari ya zamanto shi kadai ake gani a wurin taron, wallahi mun san ba yadda za’a yi a tashi daga taron nan na Sakkwato, ba tare da an kawo wani abu na hassada da gaba da kiyayya game da Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II ba.
Sun manta, shi Muhammadu Sanusi II ikon Allah ne. Idan ba haka ba, ku duba ku gani, kwana hudu kawai yazo yayi a Najeriya, amma duk ya rikitasu, ya firgitasu, ya dimautasu. A yau gashi kwanansa biyar kenan da komawa Ingila, shi yana can yana harkokinsa, bai ma san da su ba, amma anan ya bar su da jimami, kuma ya cusa masu bakin ciki da damuwa. Ina rokon Allah ya karawa Sarki sutura, kwarjini da imani, amin.
Shi yasa ni har kullun, nike fadawa mutane cewa, a gaskiya wadannan miyagun mutane, da haushin Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II zasu mutu (wato kare zai mutu da haushin kura kenan). Domin ni na ga cewa kullum hankalinsu sai dada tashi yake yi akan lamarinsa. Sun kasa samun natsuwa gaba daya a rayuwarsu. Allah Sarki, Muhammadu Ikon Allah!
Kuma babban abun tambaya anan da kowa ya kamata ya tambayi wadannan mutane shine, wai shin su mutanen Gwamnatin Jihar Kano basu da wani aiki ne, duk sun gama kaf, sai hassada da adawa da Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II? Kai jama’ah, ya Allah ina rokon ka, ka cire muna ciwon hassada a tsakanin mu, amin.
Amma idan ba haka ba, ta yaya za’a ce kun zama gudanar da gwamnati kawai a wurin ku, shine yin gaba da kiyayya da Sarki Muhammadu Sanusi II. Komai ya tsaya cak, an dakatar da yiwa talakawan jihar Kano abun da ya kamata, an koma koda yaushe ba abun yi sai firar Sarki Sanusi II, a gidan gwamnati da sauran wuraren taruwarku.
Yanzu jama’ah ku duba don Allah, idan ba rashin tarbiyyah ba, ta yaya za’a ce, wai kwamishinan addinai na Jihar Kano (Ko kuma Kwamishinan lalata harkokin addinin Musulunci na jihar Kano), wanda ake yiwa lakabi da Baba Impossible, ya tashi cikin rashin ladabi, da rashin da’a, da rashin biyayya; babu kunya, babu tsoron Allah, babu kunyar mutane, babu girmama na gaba, ya tashi a gidan Gwamnatin Jihar Kano, a gaban Gwamna Ganduje, wanda suke cutar addinin Musulunci, suna yiwa mutane karya, wai suna yi masa lakabi da Khadimul Islam, shi wannan kwamishina ya tashi yana kalubalanta tare da tambayar Khalifan Shehu Ibrahim Inyass, wato Sheikh Mahiy Inyass, yana cewa wai me yasa suka nada Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Khalifan Shehu Ibrahim Inyass a Najeriya. Duk duniya ta shaida wannan rashin mutunci da ya faru, a lokacin da tawagar Shehu Mahiy Inyass din suka kai ziyara gidan Gwamnatin Jihar Kano, a ranar Alhamis, 18/03/2021, a inda aka shirya masu walimar cin abinci. Da ma shi wannan Kwamishina, Baba impossible ashe sun shirya walimar ne a karkashin ofishinsa, ba don komai ba, sai don a kalubalanci Sheikh Mahiy Nyass, domin kuma ayi amfani da wannan dama a soki Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi ll, kuma wai a kunyatashi a idon duniya!
Amma su iyalan Shehu Ibrahim Nyass, don su nuna masu cewa, su ba shashashu bane irin su, kuma ba zasu taba yarda a siyasantar masu da sha’ani ba, sai wani jikan Shehu Ibrahim Nyass, Dan Sayyada Aisha Inyass, wato Shehu Tijjani Sani Auwalu, ya mayar masa da martani a nan take, ya fada masa cewa, ai wannan ba maganar nan wurin bace, don haka Khalifah ba zai yi wannan magana a nan ba. Alhamdulillah, mun gode Allah akan wannan.
Kuma shi wannan Kwamishinan na Ganduje, wato Baba impossible, shine fa aka ce yana daya daga cikin mutanen da suke da hannu dumu-dumu wurin yin karar marigayi Sheikh Isiyaka Rabi’u a kotu; a lokacin suka ce su basu yarda shi Sheikh Isiyaka Rabi’u din ya zama Khalifah ba, bayan nada shi da aka yi, lokacin rasuwar Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi I murabus.
Amma wai wadannan mutane, sune suka fito ayau, kuma wai suna nuna cewa su masoyan ‘yan Darikar Tijjaniyyah ne, saboda ha’inci da yaudara da suka iya. Da ikon Allah, kamar yadda basu ci nasarar wargaza Darikar Tijjaniyyah ba a wancan lokaci, haka ma ayau, Allah ba zai taba basu nasara su rusa ta ba!
Jama’ah kun dai gani ko, shi yasa, da yake su iyalan Shehu Ibrahim Nyass ba jahilai bane irin su, tuni sun riga sun gano, duk makirce-makircen da ake kullawa a Kano, wato ana nema ne a dulmuya su cikin bakar siyasar rashin mutunci irin ta su Ganduje. Don haka sai suka bi al’amarin a hankali, kuma cikin ilimi da natsuwa da hangen nesa.
Sannan na shaida maku a baya, cewa an gano wata takarda muhimmiya daga Sheikh Ahmad Tijjani Nyass, zuwa ga Mai Martaba, Sarkin Kano, Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, wadda take labarta muna matsayin Sarki Muhammadu Sanusi II, da girmansa da mukaminsa, da ko shi wanene a cikin Darikar Tijjaniyyah, tun a shekaru bakwai da suka gabata. Wato ina nufin tun lokacin da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kaddara masa zama Khalifan Khalifah Sir Muhammadu Sanusi I. Mai Martaba Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II ya kasance Mukaddamin Darikar Tijjaniyyah ne, Khalifah, kuma Batijjane na gaske, babu kokwanto ko kadan a cikin wannan. Don haka duk masu jayayya su daina daga yau, domin kuwa komai takamar mutum a cikin Darikar Tijjaniyyah, kuma komai dadewarsa a cikin ta, kakansa bai zama Khalifan Shehu ba, kuma shi bai hau kan daya daga cikin kujerin Sarki Khalifah ba. Saboda haka, ya kamata kowa ya farka, kowa ya bude idonsa, domin ya fahimci irin matsayin da Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II yake da shi, da kuma irin girma da amanar da suke kansa, na kasancewarsa uba kuma jagora ga dukkanin wani basarake na kasar Kano, kuma uba ga kowane Batijjane da ma wanda ba Batijjane ba da yake kasar nan. Ina rokon Allah ya taimaki Sarki Khalifah Muhammadu Sanusi II, amin.
Kuma har kullun, muna ta kara tunatar da al’ummah cewa, shi fa Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II ba wani abu ne ya jawo masa irin wannan kauna da soyayya a wurin dimbin al’ummomin duniya ba fa illa dabi’unsa masu kyau, da kuma halayensa nagari. Wallahi duk wanda yasan Sarki Muhammadu Sanusi II, kuma yayi mu’amala ko wata hulda da shi, to zai san da haka. Misali, ga kadan daga cikin halayensa da dabi’unsa:
Da farko dai shi Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, mutum ne mai dimbin ilimi, na addini da na zamani, mutum ne mai biyayya da da’a ga Allah da Manzonsa (SAW). Sannan shi mutum ne mai da’a da biyayya ga iyaye da kuma dukkanin magabatansa. Shi mutum ne mai hankali, mai hakuri da yafiya, kuma shi mutum ne mai neman kyakkyawan sakamako a wurin Allah Subhanahu wa Ta’ala a koda yaushe. Shi mutum ne mai yin abu domin Allah (wato da ikhlasi), mai kyakkyawar mu’amala ne ga mutane da kuma iyalan gidan sa. Mutum ne mai son ayi gyara a koda yaushe, mutum ne shi mai umurni da aikata kyakkyawan aiki da kuma hani akan aikata mummunan aiki. Sarki Sanusi mutum ne mai son tsarki, mai tsafta, sannan shi mutum ne mai yawan kiyaye harshensa daga surutu da maganganun banza marasa amfani, sai fa idan a wurin fadin gaskiya ne, ko kuma kare hakkin marasa karfi, to anan kam ba zai yi shiru ba. Sarki Muhammadu Sanusi II mutum ne mai yawan Ibadah da bautar Allah, mutum ne mai tausayi da saukin kai, mutum ne da Allah yayi masa kyawon sura da kyawon halitta, mutum ne mai tsantseni game da rayuwar duniya, mutum ne da baya hana abun da aka tambayeshi, sai fa idan baya da shi, mutum ne mai karfin imani da tawakkali, mutum ne mai tausayi da son yara, mutum ne mai yin rangwame ga mutane, sannan shi mutum ne mai tsoron Allah da kamewa.
Ya ku jama’ah, wallahi Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II mutum ne mai ciyar da abinci ga mabukata, mutum ne mai son taimako, mutum ne mai fadin gaskiya komai dacinta, kuma ko meye zai same shi akan hakan ya yarda. Shi mutum ne mai kokari wurin girmama iyakokin Allah, mutum ne mai sakin fuska ga mutane, mutum ne mai rikon amana da cika alkawari, mutum ne jarumi, mai jarumta da rashin tsoro ko kokwanto, mutum ne mai karamci da jurewa akan haka, kuma shi mutum ne mai kunya.
Ya ku bayin Allah, Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II mutum ne mai kankan da kai, mai tawali’u, kuma shi mutum ne mai nuna rahama, tausayi da jin kai ga talakawa, kuma mutum ne mai saukin kai. Sarki Sanusi II mutum ne mai yafiya da hakuri kuma adali, mutum ne mai tsananin tsoron Allah, kuma shi mutum ne mai wadatar zuci da hakuri da kadan.
Daga cikin dabi’un Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, ya kasance shi mai son yin alheri ne ga kowa, kai hatta ma makiyansa. Sannan sai kusancinsa ga fadawansa da talakawansa da kuma cudanya da su, da sauraren koke-koken su. Sannan sai kokarinsa wurin zuwa gayar da marasa lafiya da ziyararsu, da biya masu kudin maganinsu, kuma yayi masu alheri, musulmi ne su ko kuma wadanda ba musulmi ba. Sannan sai rashin girman kan sa, da yin godiya ga duk wanda yayi masa alheri, da kuma kokarin saka masa shi ma, da irin abunda zai iya. Shi mutum ne mai son dukkanin wani abu mai kyau da tsabta da kuma kamshi, wato mai mu’amala ne da turare. Shi mutum ne mai son shiga tsakanin masu husuma, da kuma kokarin yin sulhu a cikin dukkanin ayyukan alheri. Shi Mutum ne mai kokari wurin yiwa kansa hidima.
Jama’ah, wadannan kadan ke nan daga cikin halaye da dabi’un Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, wadanda duk wanda yayi hulda da shi, ko yake hulda da shi, to zai shaida hakan. Kuma wadannan dabi’u na gari da halaye masu kyau, sune suka sa kowa-da-kowa yake kaunarsa, kuma yake son sa tsakani da Allah. Don haka duk wata adawar makiya ba zata taba yin tasiri akan sa ba. Zasu yi su gama, daga karshe kuma sai Allah ya kunyata su kuma ya tozarta su.
Ya ku ‘yan uwa, daga karshe, muna kara jaddada godiyarmu ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan karamci da baiwa da yayi muna, ta karrama masoyinmu da dimbin masoya a ko wane bangare da ko wane sashe na duniya. Alhamdulillah, alhamdulillah, alhamdulillah.
Mun san cewa da ikon Allah, babu wani Dan siyasa, ko shi waye da zai iya tara dimbin mabiya da dimbin masoya, kamar yadda Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II zai tara. To wannan ma wata falala ce da Allah yayi masa, kuma ita suke jin haushi da hassada. Don haka wannan daga Allah ne, kuma na san babu mai iya ja da ikon Allah, sai wanda yake wawa, mahaukaci, jahili kuma dibgagge!
Sannan bayan wannan, ya kamata duk masoyin Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II yasan cewa bamu yarda wani yayi batanci ko ya nuna raini ko nuna rashin girma ga ko wane mutum ba, musamman ma Shehunnai da malamai, wai da sunan kare Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.
Kowa ya sani, babu mai iya shiga tsakanin Shehu Dahiru Usman Bauchi da Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II. Tare suke, kuma suna kaunar junansu, kuma suna girmama juna, suna kare mutuncin juna. Sarki Muhammadu Sanusi II ya dauke shi a matsayin uba, kamar yadda kuma ya dauki marigayi Khalifah Sheikh Isiyaka Rabi’u a matsayin uba, kuma mai bashi shawara irin ta iyaye. Don haka kar ku yarda wasu shedanun mutane su sanya maku wata shubuha, su nuna cewa kamar tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi II da wasu mutane akwai rashin jituwa, karya ne, babu komai tsakaninsu. Shi dai Sarki na kowa da kowa ne, baya kin kowa, kuma baya fada da kowa. Wadanda suke jayayya da ikon Allah sune suke fada da shi, shi kuwa bai san ma suna yi ba.
Maganar nada Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Khalifah, ba daga bakinsa aka ji ba, a’a, ta fito ne daga bakin Shehu Makkiy Nyass. Shi kuwa Shehu Makkiy Nyass ba zai taba yin wannan furuci ba sai da izinin Shehu Mahiy Nyass da sauran ‘yan uwansa iyalan Shehu Ibrahim Nyass. Kawai dan lokaci ne ake jira, domin ai dai anyi mai wuyar tun da har an kai ga furtawa, kuma an bayyana.
Don haka idan wasu makafi, dibgaggu, kidahumai, sun zo sun ce maku su basu ga hasken rana ba a lokacin da kowa ya gani, to ba wani abun mamaki bane, sai a kyale su da makantarsu, mu kuwa sai mu shagaltu da kallon hasken alkhairi da muke ta gani a koda yaushe.
Don Allah jama’ah, in ban da abun mamaki, wai sai an yaki Sarki Muhammadu Sanusi II ta ko halin kaka, Shehunnan Darikar Tijjaniyah sun shirya Zikirin Juma’ah a Masallacin Kofar Mata, amma Gwamna Ganduje yayi amfani da Isa Pilot da Ibrahim Shehu Dahiru Usman Bauchi, domin a canza wurin yin zikirin zuwa Gidan Sarki, kawai wai dai domin a nuna wa duniya cewa, Aminu Ado shine Khalifan Tijjaniyyah, ba Muhammadu Sanusi II ba.
Shine ganin haka su kuwa majalisar Shura na Darikar Tijjaniyyah, da Shehunnan Kano baki daya (Allah ya saka masu da alkhairi, amin), suka kauracewa zikirin gidan Sarki, suka shirya nasu a masallacin kofar mata, kamar yadda aka yi sanarwa. Wanda wallahi hakan da suka yi shine daidai, kuma sun yi abunda ya dace, kuma wallahi sun burge kowa, domin sun nunawa duniya cewa, su domin Allah suke yin al’amarin su, ba don abun duniya ba. Kuma sun nuna basu yarda a siyasantar da wannan al’amari na zikirin juma’ah ba!
Haba jama’ah, wallahi na fada maku cewa, wadannan mutane suna fada ne fa da ikon Allah. Basu damu ba, su a shirye suke su sayar da ‘yanci da mutuncin gidan Malam Ibrahim Dabo, saboda abun duniya, da kuma nufin wai a yaki Sarki Muhammadu Sanusi II, a kunyata shi. Sun manta da cewa, yakar Sarki Muhammadu Sanusi, wallahi yakar gidan Malam Ibrahim Dabo ne baki daya. Amma babu komai, shi kadai yafi karfinsu wallahi.
Ku duba ku gani, Ganduje dai a halin yanzu kowa ya fahimci cewa masarautar Kano tana aljihunsa ne, shi yasa zikirin juma’ar ma da ya tursasa, da karfi da yaji sai anyi a fada, sam babu wanda yaje, mutane sun watse, sun ki zuwa, saboda su tsira da ‘yancinsu da kuma mutuncinsu, kuma su nunawa duniya cewa, su fa suna tare da Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II.
Shehunnan Darikar Tijjaniyyah na Najeriya gaba daya, wallahi wannan kalubale ne a gare ku. Duniya ta zuba maku ido tana kallon ku. Idan saboda kawai a yaki Sarki Muhammadu Sanusi II, kuka yarda aka wargaza tafiyar Darikar Tijjaniyyah a Najeriya, to tabbas kun yi abun kunya. Ya zama dole, kuma wajibi a gare ku, ku nunawa Ganduje cewa bai isa ba. Ku nuna masa cewa ku masu ‘yanci ne. Ku nuna masa cewa magabatanku da suka kafa Darikar Tijjaniyyah ba su kafa ta ba ne saboda abun duniya. Kuma idan har kuka bari Ganduje yayi amfani da wasu tsiraru daga cikin ku, ya wargaza tafiyar Darikar Tijjaniyyah, kamar yadda yayi amafani da wasu ‘yan tsiraru daga cikin zuri’ar Malam Ibrahim Dabo ya wargaza su, to laifin ku ne, kuma hatta jikokin ku zasu yi Allah waddai da abunda kuka yi!
Ina rokon Allah ya sawwake, kuma Allah yasa ku fahimci gaskiyar da muke fada maku. Ina rokon Allah ya ba mu rai da lafiya, da nisan kwana, amin.
Wassalamu alaikum,
Dan uwaku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button