Addini

Sheikh Bala lau Yayi Martani Mai zafi Game da Masu Zagin Sahabbai

Advertisment

Ba Za Mu Sake Yarda Wani A Kowace Jiha Ya sake zagin sahabbai ba-sheikh bala lau
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce daga yanzu ahlussunnah ba za su bari wani ya fito haka kurum ya na zagin sahabbai a kowace jiha a Najeriya ba. Imam Bala Lau da ke gabatar da fadakarwa a masallacin marigayi Sheikh Alhassan Sa’id Adam a Jos jihar Filato, ya nanata yabo ga gwamnati da al’ummar don dakatar da wani mai fakewa da yin wa’azi ya na cin mutuncin sahabbai da taba janibin manzon Allah.
Sheikh Bala Lau ya nuna farin ciki yanda malamai a Kano da sauran sassa su ka hada kai fiye da yawanci lokuta a baya wajen kare sunnah. Shehun malamin bai kammala ba sai da ya nuna takaicin yanda Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ki bin hadewar JIBWIS kamar yanda ya nemi a yi, ya na mai cewa har yanzu a shirye Izala ta ke don sake karbar Sheikh Sani Yahaya da jama’ar sa a kan bin tafarkin sunnah na gaskiya.
Iman Bala Lau ya ce tun taron na Ahlusunnah COAN da a ka yi a Lagos ya kan aikawa Sheikh Sani Yahaya takardar gaiyata amma bai taba mutunta gaiyatar ba, inda shi kuma Sheikh Sani bai taba gaiyatar sa zuwa wa’azi ba ko sau daya.
Tuni malamai da dama da su ka yi karatu mai zurfi a jami’ar musulunci ta Madina irin su Saifuddeen Yakubu Musa su ka gabatar da wa’azi da a masallatai da dama, inda aka karkare a masallacin marigayi Sheilkh Alhassan Sa’id Jos. Filato na daga manyan cibiyoyin kungiyar da ke da mabiya a ciki da wajen Najeriya har da nahiyar turai da sauran sassan duniya.
Jibwis Nigeria
[email protected]
30-Rajab-1442
14-March-2021

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button