Gwamnatin Jahar Sokoto Zata Inganta Almajiranci Irin Na Kasar Indonesia
A kokarin da da Gwamnatin jahar Sokoto ke yi na inganta tsarin karantarwar makarantun Allo zuwa irin tsarin koyarwa na kasar indonesia, inda za’a hada karatun kur’ani, karatun zamani, sana’a da kuma tarbiyya a wuri daya.
Anyi shekara biyu ana tsare-tsaren ai watar da shirin, inda ranar Laraba 17/02/2021 akayi taro, taron wanda ya samu halartar masu ruwa da tsaki a kowa ne bangaren da ya hada bangaren Gwamnati, iyayen kasa, kungiyoyin da bana Gwamnati ba,malamman makarantun Allo, limamai, kungiyoyin A
addinin musulunci da sauran su.
A Lokacin taron, kwamitin da aka dorawa alhakin tattaro bayanan yadda Za a aiwatar da sha’anin ya gabatar da rahoton sa, tare da gabatar da wasu kasidu.
Mai girma Gwamnan jahar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya bada tabbacin aiwatar da muradun da ake bukata da kuma bada tabbacin kara inganta tsarin Almajirci da kuma tallafawa Makarantun da malamman su.
Hakama mai martaba Sarkin Musulmi muhammad Sa’ad Abubakar ya bada tabbacin bibiyar lamarin dan ganin an aiwatar da rahoton, wakilin ministan ilimi, da hukumar bada Ilimi bai daya nada cikin wadan da suka maganta tareda bayyana hubbasar da Gwamnatin tarayya ke yi da nuna goyon bayan su ga shirin.
Ma’aikatar Ilimi ta jahar Sokoto ta hukumar ilimin larabci da addinin musulunci karkashin jagoranci Sakataren zartarwa Dr Umar Altine Dandin mahe, hukumar Zakka da wakafi ta jihar karkashin jagoranci Shugaban zartarwar hukumar Mal. Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sokoto da hadin guiwar Asusun tallafin karatu na jiha ne suka shirya taron.
Daga: Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.