Mijin Zahra Buhari ya nuna hotunansa tare da zakin da yake wasa dashi a gida, ya jawo cece-kuce (hotuna)


Surukin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Ahmad Indimi dake auren Zahara Buhari ya bayyana hotunan zakin da yake kiwo.
Myrablac: “Yanzu wasan Egungun kake, sai ka kiyaye ko kuma ka tafi cikin sauki”
Amounalemouna: “Dubi yadda tsoro ya cika idanun ka. Tazarar da kake bayarwa ma tukuna.”
Wata Lilvicky68 a majallar Nairaland ta ce, “Ina fatan zakin ya dan bashi cizon soyayya.”
Wani memban mujallar mai suna Wallade, ya ce, “A cikin kasa mai hankali, Hukumar Kula da Dabbobi ko Kungiyar Kare Hakkin Dabbobi ne za ta dauki dabbar daga inda take tsare, da yardarsa ko ba tare da izininsa ba.
“Babu wanda ke da hakkin kiyaye dabba mai hadari kamar zaki a matsayin dabbar gida. Dabbar na gidan kallon dabbobi ne ko na daji.”
View this post on Instagram