Addini

Kotu ta amince a yi Muƙabalar Malam Abduljabbar da Malamai

Advertisment


Lauyan nan Barista Ma’aruf Yakasai ya janye buƙatar dakatar da Muƙabala da ya nemi kotu ta yi a kwanakin baya.
A baya dai Barista Yakasai ya nemi, kotun majistiri mai lamba 12 da ke gidan Murtala da ta sanya shi cikin waɗanda ake shari’ar da su, sannan ta dakatar da muƙabalar malamai da Malam Abduljabbar Kabara da Gwamnatin Kano ta shirya.
To sai dai a zaman kotun na ranar Litinin lauya mai kare Ma’aruf Yakasai, Barista Lukman Auwal Abdallah ya janye dukkan ɓuƙatun da suka nema a baya.
Da yake zantawa da Freedom Radio bayan kammala zaman kotun, lauyan ya ce, sun janye buƙatun ne la’akari da sha’awar da mutanen Kano suka nuna na a gudanar da muƙabalar.
Aƙarshe kotun ta amince da janye buƙatun da lauyan ya nema.
Harkawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto ɓangaren Gwamnatin Kano bai ce komai ba kan lamarin.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button