Labarai

Rochas Okorocha Zai Gina Makarantu Allo Irin Na Zamani Guda 6 A Jahohin Arewacin Najeriya

Advertisment

Tsohon gwamna jahar Imo Rochas Okoracha zai gina makarantu allo irin na zamani guda 6 a jahohin Arewacin Najeriya domin inganta hanyoyin neman ilimin addini.
Jahohin da za a gina wadannan makarantu sun hada da Bauchi, Kano, Katsina, Yobe, Borno da kuma jahar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana cewa wadannan makarantu ba ilimin addinin musulunci kadai za a koyarda wadannan yara ba, har ma da ilimin zamani, wato ilimin boko don ganin wasu daga cikin su sun zama Likitito, Lauyoyi, Malamai, Injiniyoyi kamar sauran ya’yan masu kudi.
Gwamnan ya bayyana cewa za a dinga koyar da wadannan yara kyau ne, sannan za a basu dukkanin kulawar da ta dace don ganin an inganta rayuwar wadannan yara.
Hakika wannan namijin kokari da Rochas yake kokarin yi wani abin a yaba masa ne, sannan wani abin kunya ne ga gwamnonin Arewa masu kokarin hana karatun addinin musulunci a maimakon su fito da irin wadannan hanyoyi da Rocha ya dauko.
Ubangiji Allah ya biya masa da bukatocinsa na alkairi.
Daga: S-bin Abdallah Sokoto

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button