Labarai

Na Rantse Da Alkur’ani Ba Ni Da Hannu Cikin Matsalar Tsaron Da Ta Addabi Jihar Zamfara Daga Bakin Gwamna Matawalle (bidiyo)

Ya kuma kalubalanci manyan jihar, sarakunan gargajiya, daidaikun al’ummar Jihar, da su fito su rantse da Al’kur’ani matukar sun tabbata ba su da hannu a matsalar tsaron jihar
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawallen Maradun ya bukaci duk wani dan jihar wanda yace yana bukatar a Kawo karshen matsalar tsaro, daya fito ya rantse da Alkur’ani cewa bashida hannu cikin Harkar, idan da gaske ne.
Bello yayi wannan kiran ne a lokacin da aka bashi sarautar hadimul Kur’an, Wanda kungiyar mahadatta Alkur’ani suka bashi a jiya lahadi a gidan Gwamnatin jihar Zamfara dake gusau .
Ya kara da cewa idan da gaske ne ana so a kawo Karshen matsalar tsoron da ke addabar Al’umma jihar, ya ce tun daga Tsohon gwamnan jihar, Yariman Bakura da Janar Aliyu Gusau da kwamishinoni da sarakuna da duk wani dan siyasa har kansila dake jihar da ya fito ya dauki Alkur’ani ya rantse cewa bashi da hannu cikin matsalar tsaron jihar.
Gwamnan ya kalubalanci yan jihar kan cewa duk Wanda ya isa a jihar ya fito ya bayyanawa Al’ummar jihar tabbacin cewa ba shida hannu, ya kuma bukaci kowa ya fadi abinda ya faɗi a lokacin yin rantsuwar kamar haka, inji shi.
“Ni Bello matawalle idan ina da hannu ko ina tare da wadanda suke da hannu ko Kuma ina taimakawa wadanda suke da hannu ko nasan wadanda suke da hannu cikin wannan matsala na rashin tsaro ina rantsuwa da Alkur’ani Allah Ubangiji Kada ya ɗahirta mani ko na sakon daya ” inji shi
Gwamnan ya Kuma bayyanawa Al’ummar jihar da cewa wajibine duk wani wanda yake aiki karkashin wannan gwamnati daya tafi filin da ake Wa’azin mako mako ya yi rantsuwa idan bashi da hannu cikin wannan Harkar.
Ya kuma bukaci malaman jihar da su kira kowa ya fito don yin irin wannan rantsuwar, ya kuma kamata daga yanzu duk wani dan siyasa mai son kujera to Sai ya fito yayi rantsuwa kafin a tsaidashi a siyasance.
Ga bidiyon nan sai ku saurara kuji daga bakinsa
https://youtu.be/5FCnpuVjiTo

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button