Murja ta Zagi iyayenta akan Mr 442
Tunidai Lokacin da labarin kama mawaki mr442 da abokinsa ola of kano ya bazu a Shafukan Sada Zumunta Wanda Murja Ibrahim itace wacce ta fara bayyana rahoton a Faifan Vedion data wallafa a shafinta na Tiktok.
An bayyana cewa an kama sune da laifin yin takardun shaidar zama dan kasa na Kasar ta Niger ta gurbatacciyar hanya wanda sunso suyi amfani da hakan domin Zuwa kasar turai, amma hakarsu bata cimma ruwa ba.
Shine murja Ibrahim kunya take Maryani mai zafi kan masu jindadi cikin bayyanin har ta zagi iyayenta bata sani ga abinda take cewa.
” Kuma ku rubuta ku aje masu wannan cece kuce kana mr 442 idan ya fito da koshin lafiya bi’izzinillahi saboda nasan ko waye mr442 musulmi ne mai kaunar ibadar Allah in sha Allahu zai fito lafiya, sai dai kuga cigabansa ba dai ci bayansa ba bi’izzinillahi.
Kuma billazillahi sai kunyi kuka da idanunki idan mr 442 ya dawo lafiya lau da kuke cewa yayi kaza yayi kaza na farko dai mr 442 bai dauki yar ku ba.idan kunce mr 442 yana lalata yar mutane akwai wadda yace dan Allah dan Annabi kizo inda nake zanyi lalata da ke ko in nuna miki hanya ta lalata?.
“Ko kuma akwai yar 442 yaje har gidan ubanta iyayenta suna janta 442 yana janta ya tafi da ita cewa zai lalata ta? Duk wadda kunga gani ta samu taje inda 442 kafin ta samu taje inda yake ba karamar shan wahala tayi ba. Su da kansu suke kai kansu da kansu, Sa’a nan 442 da kunne na yake cewa murja ni ina jin tsoron masu kirana cewa zasu zo inda nake.
“Yau ke kai idan kunba yar ku tarbiya ko kuma ka bar yarka Tarbiya shin zata tashi taje waje 442? Tarbiyarka ce tayi kadan a gida ko kuma shiryar da kake yi akanta yayi kadan yunwa ta isheta, baka tarbiyantar da ita ba shiyasa har ta samu damar zuwa inda mr 442 amma da ka bata tarbiya mai kyau ka kula da ita bazata je tabi hanyar inda su mr 442 suke ba. Kai ne da kanka ka kai ko kuma kece da kanki kika lalata tarbiyyar yarki/ka ba 442 ne ya lalata maka ƴa ba.
Idan yanzu baza yi addu’a akan halin da su 442 suke ba kaja bakinka kayi shiru.”
Ga bidiyon nan ku saurari cikakken bayyani daga bakinta hausawa kance waka a bakin mai ita yafi ɗaɗi.