Labarai

Rahoto na musamman: Zamfara 02: Sulhu Shi Kadai Ne Mafita – Yadda Malam Dr Ahmad Gummi Ya Shiga Dajin Sububu Da Dajin Pakai A Garin Shinkafi (Hotuna)

Sama Da Samari 500 Masu Dauke Da Makamai Malam Ya Gana Da Su ~ Dr Ahmad Gummi

Advertisment

…SAMA DA SAMARI 500 MASU DAUKE DA MAKAMAI MALAM YA GANA DA SU.
… MUN BIYA KUSAM MILIYAN 200 KUDIN FANSA, DA MATA KUSAN DARI HUDU DA AKA KASHAWA MAZAJE – Chairman Shinkafi
…SULHU BA ZAI YUWUBA SAI AN DENA FARANTAR ‘YAYAN FILANI – Muhammad Bello (Kwamandan Dajin Sububu)
…MU YARAN BUHARIN DAJI NE, IDAN AN KASHE ZA’A SAMU SABABBIN DAMA SAMA DA 30 – Alhaji Turji (Kwamdan Dajin garin Pakai)
… WALLAHI TAFIYAR NAN BABU SIYASA A CIKI MUNA SON GANIN AN KAWO KARSHEN ZUBAR DA JINI NE – Alhaji Shehu Buba
…SULHU WAJIBI NE, KU RUNGUME SHI DON KAWO KARSHEN KASHE-KASHE – Sheikh Sanusi Kutama
…ALLAH MUKE NUFI DA WANNAN AIKI, KU ZAMA KHALIFOFIN ALLAH NA GARI WANNAN DAJIN NAKU – Sheikh Dr. Ahmad Gumi
A rana ta biyu 02/02/2021 cikin kokarin da Sheikh Dr. Ahmad Gumi yake yi na ganin Allah ya dawo da zaman lafiya a tsakanin Fulani da jama’ar gari, malam ya samu damar shiga Karamar Hukumar Shinkafi a jihar Zamfara inda yake ziyara na kwanaki biya da kuma amsa gayyatar gwamnan jihar Zamfara Matawallen Maradun domin ganin kokarin da gwamnatinsa take yi don ganin ta tsugunar da fulani a inda ta gina musu.
Bayan da tawagar malam ta karya da misalin karfe 11 na rana muka kama hanya sai fadar Sarkin Shinkafi inda muka dauki tsawon awa daya da rabi kafin mukai fadar.
Isarmu ke da wuya mai martaba sarkin Shinkafi ya fito da tawagarsa suka karbi Malam hannu bibbiyu, inda da farko aka karanta Alkur’ani mai girma daga bakin Alarammomi da muke tafiya da su, inda malam Nasiru Ayuba (Dan agaji) ya gabatar da manyan mutanen da suke yiwa malam rakiya tare da makasudin zuwanmu wannan masarauta.
Sheikh Dr. Ahmad Gumi wanda ya yi cikakken bayanin dalilin zuwan mu wannan gari da kuma nufinsa na shiga cikin daji domin ganawa da kwamandojin dajin don fada musu kalmomin Allah da kuma nuna musu matsayin zubar da jini da kuma hanyoyin da ake fata idan aka bisu Allah zai bada dawwamammen zaman lafiya a masarautarsa.
A nashi jawabin Sarkin Shinkafi yayi godiya ga Allahu Subhanahu Wata’ala da Allah ya albarkace su da zuwan malam da tawagarsa, ya fadawa malam irin zaman lafiya da aka samu tun bayan zuwan Gwamna Matawalle a matsayin gwamna, da kuma aminci da Fulani suke da shi a wannan yanki nashi.
A nashi Jawabin Chairman na karamar hukumar Shinkafi ya yajjada kalaman Sarkin Shinkafi inda ya tabbatarwa da Malam tsawon watanni shidda ba su sami rahoton daukar wani ko kashe wani ba saboda irin zaman lafiya da suke yi da fulanin yankinsa.
Sai dai a nasa jawabin yayi korafi game da yadda ake karyawa fulanin alkawarinsu da kuma rashin samun amincewa idan suka yarda aka yi sulhu ya bayar da misalin wanda ya ajiye makami daga baya ya shigo kasuwa hukuma ta kama shi ta kashe.
Ya fadi irin rashin zaman lafiya da garin Shinkafi yayi a waccan gwamnatin da ta wuce inda yace sun biya kudin fansa masa da miliyan dari da casa’in da bakwai, mun samu marayu sama da dari shiga, mata dari uku da saba’in da uku da suka rasa mazansu.
Gamawarmu ke dawu muka samun tabbacin gayyatar wadannan kwamandojin dajin inda suka bayar da sharadin cewar motoci biyarne kawai suke bukatar shigowa inda suke. Sannan da sharadin basu yarda wani jami’i ko daya ya taka dajin nasu ba.
Bayan da aka gama shiye-shiye da zaban wadanda zasu yiwa malam rakiya, muka kama hanya inda muka yi tafi ta a kalla kilomita 15-20 kafin isa murinsu.
Bayan Babban Limamin Sultan Bello ya bude taro da Addu’a da fatan Allah ya albarkaci abinda da za a tattauna, Malam Nasiru ya gabatar da malam da tawagarsa inda ya mika abin magana ga Muhammadu Bello.
A jawabinsa Bello wanda ya fara da baiwa malam hakuri game da tsaiko da aka samu kafin su sami damar shigowa yace saboda rashi sanar da su akan lokaci ne, inda ya baiwa malam shawara ga shiryawa sosai da bayar da sanarwa kafin a zo domin su tara nasu jama’a sosai.
Ya yi magana a madaddin kwamandojin dajin, inda yace tun daga lokacin da aka zauna da su cikin daji domin yin sulhu basu karya wannan sulhunba kasancewar wannan gwamnatin ta fito da wadansu hanyoyi da suka taimaka wurin kawo zaman lafiya.
Daga cikin korafin da yayiwa Malam bayan ya Malam ya umarceshi da ya ce duk irin ci gaba da za a kawo inda ba za a dena buge fulani ba a Jihar Zamfara idan suka shiga kasuwa ko wurin kiwo to ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba.
A nashi Jawabin Sheikh Dr. Ahmad Gumi bayan fada musu matsayin Addinin Musulunci game da daukar makami akan musulmai kuma yayi musu alkawari game da kai kokensu inda ya dace.
A nashi jawabin DPO Shinkafi ya bata tabbacin cewar suna iya kokarinsu wurin ganin an kwatowa karshen wannan matsala ta kashe yayan fulani da kuma sasanci tsakanin su da jama’ar gari.
A nashi jawabin Chairman na Shinkafi yayi musu godiya bisa hadin gwiwa da suke ba wannan gwamnatin da kuma kara tabbatar musu da cewar tunda malam ya shigo ga kuma abinda gwamnatin Matawalle take yi In Allah Ya yarda za a kara samun zaman lafiya mai daurewa.
Tun a farko sai da Alhaji Shehu Buba ya fara gabatar da nashi jawabin a harshen Fulatanci da kuma kara tabbatar musu da cewar wannan tafiyar tsakani da Allah ce babu yaudara ko siyasa ya kuma fada musu suna iya kokarin su ga an kawo karshen wannan kashe-kashen da ke faruwa a fadin Arewacin Najeriya baki daya. A karshe Malam ya raba musu littafan Ahalari da Bagadadi domin karantar da su.
Wannan dajin Sububu da muka shiga da farko sun hada a dauko komai a video ko hoto inda Kachalla daya daga cikin kwamandojin yace duk wanda ya dauki hotonsu zasu harbe shi, amma daga bisani Muhammadu Bello ya yarda a dauke shi yace daman shi ya saba magana a gaban yan jarida kuma daman shine tsani tsanin gwamnati da jama’ar Fillani.
Fitarmu ke da wuce bamu zarce ko ina ba sai cikin kurmin daji inda muka kwashe tsawo mintina 45 muna tafiya kafin mukai garin Pakai inda muka sami daba mafi girma da bantsoro da ke tsakanin Zurmi da Shinkafi inda kuka tara da samari da matasa ‘yan shekara 14 zuwa 35 sama da 500 babu wanda babu bindiga a rataye da kafadarsa, da kayan sojoji a jikinsu.
Bayan da Alhaji Shehu Buba ya gabatar Limamin Sultan Bello Kaduna Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam, ya cigaba da yanin makasudin shigowarmu wannan dabar inda ya fada musu kokarin da Sheikh Dr. Ahmad Gumi yake yi na ganin an samu dawwamannen zaman lafiya.
Da ya karbi abin magana Alhaji Turji wanda shine yayi magana a madadin kwamandojin da suka zo sauraren Malam, yayi maraba da zuwa malam da yi masa fatan alkairi da kuma amincewa da suka yi da su gana da shi da tagwarshi kasancewar babu wani alkawari da aka yi musu a baya aka cika musu. Amma da aka fada mishi cewa malamai ne zasu zo su same su sai ya ce bari su saurare su suji abinda zasu zo da shi.
Ya yi korafi sosai game da yadda aka mayar da fulani saniyar ware yadda aka talauta su da yadda aka mayar da su bari da buge su a kan hanya da rashin yarda da koda mashin ne aka ga bafillatani da shi sai ce kidnapper ne shi.
Ya fadawa malam cewar idan ba ta maganar sulhu ba babu yadda za ayi a kawo karshen wannan abu da yake faruwa, ya fada cewar Allah kadai ya san adadin makamai da suke da su da kuma abinda zasu iyayi idan suna son hargitsa jihar gaba dayanta.
Ya fadawa malam cewar kashe-kashen kwamandojin da ake yi babu wani abu da yake haifarwa illa kara samun sababbin dabba. Ya ce domin su kansu yaran Buharin Daji ne, kuma yana tabbatarwa da malam cewar shine ya datse wadannan bataliyar amma da za a kashe shi za a samu sama da karin daba talatin.
A nashi jawabin Sheikh Sanusi Kutama wanda shine wakilin Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga dukkan kwamandojin da cewar don Allah su karbi sulhu ya kuma basu tabbacin cewar wannan kashe – kashen ba zai haifar da da mai ido ba.
A jawabinsa Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya yi musu nasiha ne da cewar su kasance a matsayin kalifofin Allah na gari a bayan kasa, kada su kashe wani, kada su yi zina da shaye-shaye da kuma jawo hankalinsu game da lafin zubar da jini.
Ya kuma jawo hankalinsu game da hadisin Manzon Allah SAW da yake fadin amfani bin abubuwa da lalula da yadda suke kawo amfani a cikin kowace irin hatsani. Ya kuma rokesu game da don Allah su bayar da hadin kai da kuma yarda da cewar zasu bari a fara zuwa ana shigo daji ana karantar da su Allah da kuma koya musu addini.
A karshe malam ya raba musu littattafai da kuma atamfofi da yaduka domin kaiwa matansu da su kansu.
Cikin yardar Allah bayan rufe taro da addu’a mun fito dajin idan suka yo mana rakiya har bakin rafi daga bisani muka karasa Karamar Hukumar Shinkafi inda muka ci abinda da hutawa sannan misalin karfe 9:16 na dare muka kamo hanyar Gusau inda muka iso karfe 11:30.
Malam ya samu rakiyar Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Limamin Sultan Bello da Sheikh Sanusi Kutama, Professor Usman Yusuf, Mal Tukur Mamu, Shugaban Jaridar Desert Herald, Alhaji Shehu Buba (tsohon chairman Toro LGA, Bauchi), Wakilan Sarkin Shinkafi, Mal Sulaiman Abubakar Mahmud Gumi (Dan Majalisar Tarayya me wakiltar Gumi), Alhaji Rufa’i Chanchangi (Tsohon dan majalisar tarayya Kaduna), manyan Malamai da Alarammomi. DPO na Karamar Hukumar Shinkafi, da Chairman Shinkafi LGA, da Alhaji Moi, matashin da yayi mana jagora ya kaimu wurinsu.
Allah Muke roko da ya karbi wannan aiki da kuma karawa malam da sauran jagorori lafiya da iklasi ya bamu nasara a cikin abinda muke newa amin.
Salisu Hassan Webmaster
08038892030
03/02/2020

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button