Duk Wanda Ya Hana Aiwatar Da Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Zagi Annabi, To Ya Jira Bala’in Da Allah Zai Saukar Masa, Cewar Sheikh Sani Sharif Umar Bichi
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izalah reshen jihar Kano, Sheikh Sani Sheriff Umar Bichi ya jinjina wa Gwamna jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa jajircewa da ya yi akan wanda ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW) aka yanke mai hukuncin da ya dace da shi.
Sheik ya kara da cewa “Allah ba zai daina turo mana bala’i ba har sai mun tuba daga zunuban mu kuma mun daina zagin Allah da Manzon (SAW)”.
Sheik Bichi ya kara da cewa duk wanda ya yi sanadiyyar aka ki yin wannan hukunci sai Allah ya dora masa bala’in da ba zai taba tunani ba.
Ya kuma yi fatan Allah ya sa Gwamnatin jihar Kano ta cigaba da yanke hukunci ga duk wanda ya aikata irin wannan sabo. Kuma Alkalin da ya yanke hukuncin Allah ya shi masa albarka, Allah ka daukaka shi.
Sheikh ya yi wannan jawabin ne a karshen karatun tafsirinsa da ya gudanar a yau kamar yadda ya saba gudanarwa kai tsaye a kafafen yada labarai a gidansa dake garin Bichi a jihar Kano.
Daga karshe Malam ya yi addu’o’i na zaman lafiya ga kasar mu da jiharmu da ma Musulman duniya baki daya.