Wasu mutane sun bankawa makarantarsu Hanifa da anka binne Gawarta wuta (bidiyo da Hotuna)
Wannan hukunci da wasu matasa suka dauka rashin hankali ne ba daidai bane har a tsarin Ubangiji, domin ginin makarantar ba mallakin Abdulmalik bane, na wani bawan Allah ne ya bashi haya
Makaranta ce wanda take kusa da gidajen mutane bayin Allah, idan ansa wuta babu wanda yake da tabbacin wutar zata tsaya iya makarantar bai shafi gidan mutane ba
Duk wanda yake da hannu a lalata dukiyar wani to ya dauka wa kansa bashi da zai biya da ladansa a ranar Hisabi
Jama’a ya kamata mu kasance al’umma da take da tsari mai kyau da sanin yakamata da kuma bin doka
Allah Ya sauwake.
Ga bidiyon yadda anka bankawa makarantar wuta nan.
https://youtu.be/eYaSuAip7cc