Zabgegiyar budurwar da tayi wuff da dukulkulin saurayi ta bayyana tsabar sonsa da take (Hotuna)
So gamon jini Hausawa ke cewa kuma baya duba asali, kyau, kudi ko wani banbanci na rayuwa. Abubuwan da so ya kan duba shine dabi’a, yanayin masoyin, kankan da kai, juriya, saukin hali da sauransu da idanuwa basu iya kallo.
A yayin da wasu ke gaggawar fadawa aure saboda sha’awa, wasu suna daukar dogon lokaci wurin samun cikakkiyar yarda da juna, hakuri da kuma soyayya mai wuyar tarwatsawa.
A lokacin da hotunan Lilian Mwangi da angonta suka fada kafafen sada zumuntar zamani, jama’a suna ta dariya tare da sharrance gajeren mijinta.
Kamar yadda Legit .Angon kusan tsawonsa rabin matar ne, lamarin da yasa maza suka sha alwashin ba za su taba yin irin wannan auren ba.
Amma kuma, waye ya kafa dokar nan ta cewa dole sai miji ya fi mata tsayi? Wadannan tambayoyin ne jama’a suka dinga yi.
Lilian ta ce tana kaunar angonta Mwangi Wawira a yadda yake. A takaice tana matukar farin cikin haduwarsu a shekaru hudu da suka gabata kuma yanzu suka angwance.
Masoyan sun yi aure a 2020 inda Lilian tace “Muna farin ciki kuma muna shan amarcinmu. Soyayya babu ruwanta.”