Labarai

Nigeria Youth Investment Fund: Abu uku da suka kamata ku sani kan samun tallafin matasa N75bn

Gwamnatin Najeriya ta buɗe sabon shafin da matasa za su gabatar da ɓukatarsu ta neman tallafin kuɗi naira biliyan 75 na shirin raya matasa (NYIF) musamman masu neman tallafin bunƙasa kasuwancinsu.

Babban Bankin Najeriya ne ya ɗauki nauyin shirin na ma’aikatar ci gaban matasa da wasanni da nufin saka jari ga matasa masu tunanin kasuwanci a ƙasar domin bunƙasa tattalin arziƙi da kuma samar musu da ayyukan yi.

  • 1. Wa ya cancanta?

A bayanan da gwamnati ta fitar ta ce sai ƴan tsakanin shekara 18 zuwa 35 da suke da tunani na kasuwanci kuma suke buƙatar tallafin kuɗi ne za su iya neman wannan tallafi.

  • 2. Me ya sa gwamnati ta ƙaddamar da tallafin?

Tallafin kuɗin ya shafi zuba jari ga tunanin matasa na kasuwanci da basirar da suke da ita. Gwamnati ta yi imanin cewa za ta sauya tunanin matasan su koma dogaro da kansu ta yadda za su taimaka wa ci gaban ƙasa. Shirin na tsawon shekara uku ne.

  • 3. Ta yaya za ka samu tallafin?

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin sadarwa na intanet, Lauretta Onochie, ta bayyana cewa matasan da ke son tura buƙatarsu za su shiga wannan shafin, a nan

Amma kafin cike fom ɗin tura buƙata, dole sai mutum ya tabbata yana da lambobin banki na BVN.

Gwamnati za ta saki naira biliyan 25 duk shekara har shekara uku da za a kammala shirin.

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce matasa 500,000 za su amfana da shirin duk shekara tsakanin 2020 zuwa 2023.

Kuma ya ce shirin na gwamnatin Buhari domin magance matsalar rashin ayyukan yi ga matasa, shiri ne mai ɗorewa.bbchausa ne ta kawo wannan rahoto.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button