INNALILLAHI ! Yadda Wata Mata Tayiwa ‘Ya’yanta Yankan Rago A Kano (Hotuna)
A safiyar yau Majiyarmu ta hausaloaded ta samu wani labari daga shafin Facebook wanda dandalin dokin karfe na wallafa a shafin da wani labari mai ban mamaki da al’ajabi.
Wanda sai ya tayar maka da hankali shin jama’a kishi hauka ne?
Ga jawabin da sunka wallafa a shafin su
“A Taƙaice: Kano!
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano sun samu nasarar kama matar nan da ake zarginta da yi wa ‘ya’yanta biyu (mace da namiji) yankan rago saboda mijinta ya yi mata kishiya.
#ataƙaice”
Wannan da kunka ga an nuna da alamar arro itace matar tare da ‘ya’yanta.


A kuma wata majiya daga shafin datti assalafy ya ruwaito cewa.
“INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI’UNN
‘Yan sanda a jihar Kano sun kama wata matar aure mai suna Hauwa’u a unguwar Sagagi wanda ta yiwa yaranta biyu yankan rago da wuka ta kashe su, saboda tsananin kishi wai mijinta zai karo mata kishiya
Ance ba ta da tabin hankali, a kan kishi ne ya sa ta kashe yaran da ta haifa da mijinta wai don ta huce haushin kishi zai kara mata kishiya, wannan rashin imanin ya kai makura, ko mahaukaciya ba zata iya aikata wannan danyen aikin ba


Shiyasa kullun muke jawo hankalin ‘yan uwa matasa, kunga wadannan ‘yan mata da ba ruwansu da saka hijabi suna bayyana tudun kirjinsu da tudun bayansu kar ku bari ya rudeku, kuma wallahi kuyi hankali da aurensu
Allah Ya sauwake”


