Labarai

Abinda Ya Biyo Bayan Bude Garin Baga Na Jihar Borno ~ Datti Assalafy

Advertisment

 
Bayan da Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bude garin Baga a hukumance, ya kuma fara mayar da mutane daga sansanin gudun hijira, yanzu haka mutanen Baga suna tururuwar kai kansu daga Maiduguri zuwa garin Monguno, wanda anan ne akayi sansani sannan a wuce da su zuwa garin Baga a jerin gwanon motoci (convoy)
To amma matsalar da ake fuskanta kuma itace mayakan Boko Haram sun kafa shingen binciken ababen hawa (checking point), suna karbar kudade da wayoyi daga hannun matafiya, ana samun a kalla shingen bincike (gate) na Boko Haram har guda shida tsakanin birnin Maiduguri zuwa garin Monguno, a wasu lokutan su kan kama mutanen da suke zargin ma’aikatan gwamnati ne ko na kungiyoyin agaji (NGOs) su tafi da su jeji
Ban taba binciko wani lokaci da Boko Haram suke fama da tsananin talauci ba kamar wannan lokacin, domin idan sun tare hanyar Monguno ko naira 50 suka tarar a jikin mutum karba suke, suna kwace kowace irin waya, idan sunga rigar jikinka yana da kyau zasu karba, takalmi kuwa har da silifas karba suke, abinci, sabulun wanka, reza duk suna karba, suna caje jikin mutane maza da mata tsaf suna karban duk wani abu da suka samu su tafi dashi jeji
Amma yanzu abin yafi kamari, domin duk da wannan lamari ya kai kwana hudu yana faruwa amma har yanzu babu wani mataki da hukumomi na soja ko na siyasa suka dauka, sannan babu wata kafar watsa labarai da ta wallafa labarin, amma kowa yayi imani da cewa hakan yana wakana ga wadanda suke tashi daga birnin Maiduguri su tafi garin Monguno zasu tabbatar
Maganar gaskiya Gwamna Zulum yana kokari kuma niyyarsa mai kyau ne, sai dai bashi da sojoji bashi da ‘yan sanda, abinda yake dashi ‘yan kato da gora ne, su kuma basu da karfin tabbatar da tsaro akan hanyar Monguno balle su hana Boko Haram yiwa mutane kwace da fashi da makami
Muna jawo hankalin Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari ayi bincike a dauki matakin da ya dace, Boko Haram sun kafa shingen duba ababen hawa suna yiwa mutane fashi da makami a hanyar zuwa garin Mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro
Allah Ka kawo mana karshen wannan masifa Amin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button