Labarai

YANZU-YANZU: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero Ya Zama Shugaban Majalisar Masarautun Kano Na Har Abada

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartar da Dokar Kwaskwarimar majalisun Masarautar jihar, kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.

Majalisar karkashin jagorancin kakakin, Abdulazeez Gafasa, ta amince da gyaran ne yayin zaman majalisar na ranar Talata a Kano.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Kabiru Dashi ya ce gyaran ya yi wa Sarkin na Kano tanadin zama Shugaban Majalisar Sarakunan, na din-din don haka yanzu an kawo karshen batun karba-karba.

Sources: Rariya

A cikin sabuwar dokar, yawan masu sarautun ya kuma karu daga mambobi hudu zuwa biyar, don ba da damar gudanar da zabe cikin adalci da sabon sarki a duk lokacin da akwai gurbi.

Muna da masu rike da masarauta guda hudu a kowacce karamar majalisar masarauta, a halin mutuwa ko cirewa, muna kokarin kaucewa halin da biyu za su goyi bayan biyu kuma biyu za su ki.

Ta hanyar kara yawansu zuwa biyar;  dole ne ya zama mai gaskiya da adalci yayin zabar sarki.  Sannan kuma, sabuwar dokar za ta bayar da wa’adin kwanaki uku don zaben sabon sarki, ”inji shi.

‘Yan majalisar bayan sunyi la’akari da kwaskwarimar a kwamitin gaba daya, sun amince da kwaskwarimar kudirin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button