Labarai

Mutane Bakwai sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa a Sokoto

Akalla mutane bakwai sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale da ya faru a Dambara Lambara da ke karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani jami’in gwamnati, Ango Shagari ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin.
shafin Lindaikeja ya kara da cewa,ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon cika lodin da kwale-kwalen ya yi kuma an gano gawarwakin mutane bakwai da aka kashe kuma an binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ya kara da cewa yawancin wadanda abin ya shafa manoma ne da leburori da ke aiki a wani babban manomi a fadin kogin.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button