Labarai

Sarautar Zazzau: Tsakanin na kusa da Buhari, da abokin El-Rufa’i

Cikin mutanen hudun da Sarki ka iya fitowa, ana ganin takaran na tsakanin mutane biyu ne

– Yayinda daya cikinsu na da kusoshi a Abuja, dayan na tare da gwamnatin jihar Kaduna

– Masu zaben sarki ne zasu aikawa gwamna suna sannan ya zabi daya ciki

Rahotanni daga gidan sarautar Zazzau da gidan gwamnatin jihar na nuna cewa cikin mutane biyu za’a zabi sabon sarki; daya na kusa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma abokin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i.

Na farko, Alhaji Munir Ja’afari, mai shekaru 66, babban dan kasuwa kuma tsohon shugaban hukumar NIMASA, sannan Alhaji Ja’afaru Nuhu Bamalli, tsohon jakadan Najeriya zuwa kasar Thailand.

Yayinda Munir Ja’afaru wanda ake ganin na kusa da shugaba Muhammadu Buhari ne kuma mai da jama’a da masoya cikin manyan yan siyasa da yan kasuwa, shi kuma Nuhu Bamalli abokin El-Rufa’i ne kuma dan’uwansa na jini daga yankin Mallawa.

A gida jihar Kaduna, Bamalli wanda ya zo daga tsatson marigayi Sarki Aliyu Dan-Sidi, ya fi masoya, cewar majiya.

El-Rufa’i ya nada shi kwamishana a hukumar gudanar da zaben jihar Kaduna kuma a 2017 an nadashi Jakadan Najeriya zuwa Thailand da Myanmar da sa hannun El-Rufa’i.

Bayan haka, Bamalli ya kasance babban aminin tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.

Sanusi, wanda kuma abokin E-Rufa’i ne ya shigo Najeriya daga Ingila domin ta’aziyyar sarkin Zazzau. Amma wasu na ganin cewa ya shigo ne domin tabbatar da cewa gwamna El-Rufa’i ya zabi Bamalli.

Matsala daya da ake ganin Bamalli ka iya karo da shi shine an dade Sarki bai fito daga gidan Mallawa ba. Shi kadai ne cikin wadanda ke takara yanzu da mahaifinsa bai yi Sarkin Zazzau ba.

A bangaren Munir Ja’afaru kuwa, ya kasance na hannun daman shugaba Buhari kuma abokin manya a yankin. Legit hausa ta tattara cewa wasu manyan mutanen Arewa na kokarin tabbatar da cewa ya samu mulkin.

Wani babban jami’in gwamnatin jihar Kaduna, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa Legit hausa cewa har yanzu ba’a kaiwa gwamna sunayen wadanda aka zaba ba.

Wadanda ke zaben sarki su ne Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu; Makama Karami, Muhammad Abbas; Fagachin Zazzau, Umar Muhammad; Limamin Juma’a, Dalhatu Kasim da Limamin Kona Muhammad Aliyu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button