Labarai
Yadda zaka Cika Tallafin Kudi Kyauta Daga Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Daga 50,000 zuwa 250,000
Advertisment
Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin Jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta fito da wani sabon tsari na tallafawa kananan masana’antu da masu sana’oin hannu da kudade domin cigaba da harkokin kasuwancinsu wanda aka sakawa suna; FG MSME Survival Fund Program a turance:
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Shi wannan tsarin tallafin Gwamnati ta fito dashi ne domin tallafawa kananan masana’antu wadanda suka samu matsaloli sanadiyar annobar cutar koronabairos
Sudai wadannan kananan masana’antu da ake magana sun hada harda makarantu masu zaman kansu wato Private Schools a turance
Haka kuma tallafin ya shafi daidaikun mutane masu sana’oin hannu kamar;
Direbobin bus da tasi (Bus and Taxi Drivers)
Kanikawan mashin da motoci
Masu aikin Fulamba (Plumbers)
Masu aikin gyaran wutar lantarki (Electrician)
Masu facin mota ko mashin dama duk wani mai aikin hannu dake aiki da injimi
Karkashin wannan tsari akalla masana’antu miliyan daya da dubu dari bakwai (1.7 million) ne aka tsara zasuci gajiyar shirin
Ankasa shirin gida uku (3) kamar haka:
1. Bangaren kananan masana’antu ko kamfanoni
(Karkashin wannan bangaren akwai makarantu masu zaman kansu wato Private Schools) wanda aka sakawa suna Payroll Support Education.
Shi wannan tsarin bangaren makarantu masu zaman kansu wato Private Schools anriga anfarashi tun Jiya Litinin 21st/09/2020
2. Bangaren Sana’oin Makulashi na mata irin fanke, cincin, cake da kuma sana’ar sayarda abinci harma da hotal wanda akafi sani a turance da Hospitality Businesses
Shi wannan bangaren za’a budeshi tareda fara cikawa ranar Juma’a 25th/09/2020.
3. Bangaren gama-gari wato All Sectors a turance wanda shi kuma za’a bude tareda fara cikawa ranar Litinin 28th/09/2020.
Ga yanar gizon da za’a shiga domin cikawa:
https://survivalfundapplication.com
https://survivalfundapplication.com
Karin bayani akan tsari na farko da aka fara a halin yanzu wato Payroll Support Education:
a. Tsari ne wanda zai tallafawa kananan masana’antu kamar irin makarantu masu zaman kansu wato Private Schools da suka kasa biyan ma’aikatansu albashi dalilin rufe makarantu sanadiyar annobar Koronabairos na akalla watanni uku
Shi wannan tsarin an shiryashi akan akalla masana’antu dubu dari biyar (500,000 businesses) ne zamu amfana a duk fadin Najeriya
b. A wannan tsarin dole sai masana’anta ko makaranta tanada ma’aikata akalla uku zuwa goma (3 to 10 Staff Strength)
3. Kudin da za’a biyasu a wannan tsari zai kai dubu talatin zuwa dubu hamsin (N30,000 to N50,000)
Ababen da ake bukata makaranta ko kamfanin da zai cika ya tanada sun hada da:
1. Dole kamfani ko masana’anta ya zamo yanada rajista da hukumar Corporate Affairs Commission
2. Dole a samu BVN na shugaban masana’anta ko kamfani ko Makaranta.
3. Dole ma’aikatan kamfanin ko masana’antar ko makarantar suke akalla mutum uku ko sama da da hara har zuwa goma amma kada su kasa mutum uku.
4. Kamfanin ko masana’antar ko makarantar dole ya zamo wanda ko wacce ta mallakeshi dan asalin Najeriya ne
Muna kira ga al’ummar mu ta Arewa da ayi kokari a cika domin samun wannan garabasar. Kada mu bari a barmu a baya
Allah ya baiwa mai rabo sa’a
Kuci gaba da bibiyar shafi na domin samun sabbin bayanai akan tsarin insha Allahu
Nagode.
Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
[email protected]
Thanks
Allah saka da alheri
wallahy wannan website bayayi
[email protected]