Labarai

Jami’an KSCWC sun hallaka ‘yan bindiga 5 a garin Wagini dake ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina

Rahotanni daga garin Wagini a jihar Katsina sun tabbatar da cewa jami’an tsaron al’umma ƴan-sakai “Katsina Community Watch Corps” na ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina sun hallaka wasu ƴan ta’adda 5, a wani harin kwantan ɓaune wanda suka farmaki ƴan bindigar.

Katsina Reporters ta samu cewa, jami’an KSCWC sun ci galabar ƴan bindigar, a wani harin kwantan ɓauna da suka kai masu a daji, inda suka hallaka 5 daga cikinsu. Wanda lamarin ya faru ne, wajen misalin karfe 12pm a ranar Laraba 28 ga watan Feb. 2024.

Ƙaramar hukumar Batsari na daga cikin garuruwan da suke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina inda ake ka-she mutane tare da yin garkuwa da jama’a zuwa daji don neman kuɗin fansa.

Wani Labari :An Gwabza Ƙazamin Faɗa Tsakanin Ɓangarorin Ƴan Bindiga Biyu A JIhar Zamfara

Ƴan Ta’adda Da dama sun mutu a wani kazamar fada Da ya barke tsakaninsu a kauyen Hayin Alhaji da Dajin Munhaye Na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara ta arewacin Najeriya.

Rahotanni sun Bayyana cewa gwabzawar ta faru ne a sakamakon yunkurin da wasu ‘yan bindiga daga jihar Katsina suka yi na yin garkuwa da wasu mazauna kauyukan Zamfara a karshen makon nan.

A Cewar rahotannin bayan da ‘yan bindigar na Katsina suka mamaye kauyukan na Zamfara ne, kasurgumin dan bindigar nan na jihar Ado Alero ya yi Gaggawar kai wa kauyukan dauki don dakile Yunkurinsu na satar jama’a.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button