Gwamna Kaduna Ya Tafka Babban Kuskure Na Baiwa Yan Fim Katafaren Fili Da Kudi Domin Gina Sinima ~ Datti Assalafy
Kamar yadda BBC Hausa suka ruwaito labarin cewa; Masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood sun cika da murna sakamakon matakin da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya dauka na ba su fili da kuma kudin da za su aza ginin sinima a jihar Kaduna
Gwamnan ya ba su fili mai fadin murabba’i dubu 8000 domin gina babbar sinima ta zamani, da kuma gudunmawar kudin na fara aza harsashin ginin, a cewar wani fitaccen tauraro kuma furodusa na Kannywood, Malam Falalu Dorayi.
A cewarsa, masu ruwa da tsaki na Kannywood karkashin wata kungiya da ake kira Movie Hope ne suka nemi gwamna ya ba su filin da za su gina katafariyar sinima wadda a cikinta za a iya daukar fina-finai sannan a nuna su.
“Da ma an dade da kai masa kuka cewa akwai bukatar a samu fili a Kaduna wanda za a gina sinima, kamar yadda aka bukaci wasu gwamnoni su ma su yi a jihohinsu. Ginin zai kunshi sinima da wurin koyon sana’o’i da wurin yin daukar muryar mawaka da kuma sutudiyo, da wuraren cin abinci da wuraren shakatawa,” in ji Falalu Dorayi. ~BBC Hausa
Tsakani da Allah Malam @NasirEl-Rufai ya tafka babban kuskure da ya amince wa wadannan ‘yan nanaye masu lalata tarbiyya su samar da babban matsuguni wato sinima a jihar Kaduna, wannan babban kuskure ne
Maigirma gwamna ka sani cewa harkan film ta lalace matukar lalacewa, su da kansu ‘yan wasan kwaikwayon suke fitowa su tona asirin jununsa a kan irin lalatar da sukeyi, wata mai suna Amal ta taba zargin Hadiza Gabon da madigo wanda ta kai Hadiza gabon taci zarafinta a bainar jama’a, akwai wata mai suna Sadiya ta taba zargin wani daraktan shirin film da Luwadi, haka dai abin yake ta wakana a tsakaninsu
Maigirma gwamna kayi dubi da yadda rayuwa take kara lalacewa, muna tsoron cewa wannan guri da za’a gina a Kaduna zai iya zama babbar mahada na manyan kungiyoyin ‘yan Luwadi da Madigo da kuma cibiya na lalata tarbiyyan al’ummah
Maigirma gwamna ka tuna cewa za’a iya lalata yaran mutane a gurin, kamar yadda aka ambaci shakatawa, a asalin ma’anar shakatawa shine gurin holewa da aikata kowani irin iskanci da fasikanci da shaye-shaye, tabbas duk wata budurwa da za’a lalata a gurin, duk wani yaro da za’a lalata a gurin, duk wata matar aure da za’a kai a lalata a gurin, duk wanda ya koyi shaye-shaye a gurin zaka samu kaso na zunubi koda kuwa gurin zai shekara dubu a duniya duk zunubin da aikata a gurin kana da kaso
Maigirma gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ni Datti Assalafiy babban masoyinka ne, na baka gudunmawa tun daga 2015 har zuwa wannan lokacin, ina kare kyawawan manufofinka, ina shan zagi da tsinuwa a dalilin baka kariya da nake, kuma ina tare da kai har zuwa yau, amma wallahi bana tare da kai akan wannan abinda kayi na samarwa masu lalata tarbiyya matsugunin da zasu gina sinima
Ina son ka samu tsira a duniya da lahira, ka tuna cewa watarana zaka gushe, duniyar ma zaka bari ka hadu da Allah, ka gina abin alheri wanda lada zai dinga isa makwancinka ba wai zunubi ba, a madadin masoyanka masu kishinka muna kira gareka da ka duba illar dake tattara da samar da sanima ka janye don girman Allah
Allah Ya baka ikon fahimtar gaskiya Amin
Wallahi yan bakin ciki sai dai su mutu, da ikon allah masana'antar mu ta ci gaba kenan har illah masha allah !!! SHI MUTUM BA ZAI FADI ALKHAIRI BA SAI TSIYA