Kannywood

Da gaske ne Mahaifiyar Abba Almustapha ta rasu?

Advertisment

A safiyar jiya Asabar ne fitaccen jarumi Abba Almustapha ya wallafa hoton sa da na Mahaifiyar sa tare da wani rubutu da ya ke addu’ar Allah ya sa ta gama Lafiya, da kuma fatan Allah ya raba su Lafiya.
To sai dai, wasu kafofin yada labarai sun dauki hoton tare da juya maganar in da suka rinka yada cewar Mahaifiyar Abba Almustapha ta rasu.

Ganin yadda labarin ya ci gaba da yaduwa wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu ya nemi jin ta bakin jarumin in da ya tabbatar masa da cewar maganar da a ke yadawa ta rasuwar Mahaifiyar sa ba gaskiya ba ne.
Ya ci gaba da cewar “wannan labarin wasu ne kawai suka kirkire shi kuma ban san manufar su ta yin labarin ba.Da gaske ne Mahaifiyar Abba Almustapha ta rasu?

Ni dai na san na dora hoton mu da Mahaifiya ta ina yi mata addu’a, to ban san in da suka samu labarin Mutuwar ba, domin Mahaifiyata tana cikin koshin Lafiya a yanzu, kuma ina yi mata fatan Karin Lafiya da gamawa da duniya Lafiya, don haka ina sanar da masu yin labarin da cewar labarin da suka yada ba gaskiya ba ne, babu inda aka sanar da wannan labarin. Kuma ina addu’ar Allah ya raba ni da ita Lafiya. “

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button