Kannywood Tayi Babban Rashi ! Wanene Dauda Galadanchi ?
Alhaji Daudu Ahmad, Basarake ne, wanda ya fito daga zuriyar Galadiman Kano Abdulkadir, ya kasance mutun matukar mai mutunci, mai sanin hakkin Dan adam kuma Karimi a cikin rayuwarsa.
Alhaji Daudu sun kafa Kungiyarsu ta ‘Maitama Sule Drama Group’ tun lokacin Sarkin Kano Inuwa wato wajen 1963, hasalima sun taba gayyatar shi Sarkin Kano Inuwa inda suka yi masa ‘Stage Drama’ a gidan Makama, (Musuem) da ke Kano. Kazalika da sunan wannan Kungiya tasu suka ciwo gasar wasan kwaikwayo na dabe a Kaduna da wani wasa da suka kira shi da ‘Daukakar Musulunci’ wanda aka ba su kyautar Garkuwar Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello.
Marigayi Galadanchi, ya fito a wasu manyan Finafinai da aka yi su a nan Arewa irin su ‘Shehu Umar’ wanda aka yi adaptation daga littafin Shehu Umar wanda kuma suka yi film din a wajen 1978 a zamanin da Shehu Musa ‘Yaradua na Mataimakin Obasanjo a mulkin Soja. Haka kuma ya fito a shirin ‘Ruwan Bagaja’ na Ramalan Nuhu, wanda aka rairayo daga littafin Ruwan Bagaja na marigayi Abubakar Imam, da kuma wani fim mai suna ‘Kasarmu ce’ na Sule Umar.
Alhaji Daudu Ahmad wandae ake wa lakabi da ‘Alkali Kuliya’ ya fito a shirye-shiryen Talbijin masu tarin yawa, ya fito a shirin ‘Manta Sabo’ na NTV Kaduna (yanzu NTA Kaduna’ da shirin Taskira na NTA Kano, da shirin Kuliya na CTV Kano (Yanzu ARTV Kano) da sauran shirye-shirye masu tarin yawa.
Wannan bawan Allah na daga cikin kalilan da ya rika karbar gayyatar shirin ‘Home Videos’ ba tare da girman kai ba, daga ‘ya’yansa da jikokinsa na Kannywood. Bugu da kari Alhaji Daudu ne kadai ya samu tagomashi wajan Matasan Hausa Fim, domin kuwa su kan kai masa ziyarar girmamawa a lokuta daban-daban.
A rayuwar Alhaji Daudu ya yi Sakataren Hakimi a kasar Tsanyawa, ya yi aiki da hukumar gidan Prison (Yanzu Rehabilitation Center) a matsayin Ganduroba, ya yi aiki da hukumar tarihi da al’adun gargajiya ta jihar Kano, haka kuma ya shiga kwamitoci daban-daban a Kano Emirate council.
Babu shakka na san abubuwa da dama game da wannan bawan Allah, amma zan takaita a nan.
Allah ya jikansa ya gafarata masa ya albarkaci abin da ya bari, Allahumma amin.
-Mai Unguwa, Malam Ibrahim Mandawari.