Labarai

Batanci ga Annabi: Kotu ta hana Yahaya Sharif-Aminu daukaka kara

Yayin da ake kokarin daukaka kara kan hukuncin da aka yankewa mawakin nan da yayi batanci ga Annabi

– Kotun shari’a ta jihar Kano taki bayar da takardun da ya kamata a daukaka karar da su

Kokari na daukaka kara akan hukuncin kisan da aka yankewa mawaki, Yahaya Sharif-Aminu ya kara samun cikas a ranar Talata, bayan shugabannin kotun Shari’a ta jihar Kano sunki bayar da takardun shari’ar na gaskiya.

Sharif-Aminu wanda aka yankewa hukuncin kisa a ranar 10 ga watan Agusta, 2020, bisa laifin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW), an bashi kwanaki 30 ya daukaka kara akan wanan hukunci da aka yanke masa, hakan na nufin ranar Laraba 9 ga watan Satumbar nan ranekun zasu kare.

Kafin a amince a karbi korafin shi, ana bukatar mai lafin ya sanya hannu akan takardar daukaka karar, inda kuma za a sanya ainahin takarun hukuncin da aka yanke masa a ciki.

Sai dai jaridar Puch ta gano cewa an hana Sharif-Aminu ganin lauyansa, yayin da kuma kotun Shari’ar ta ki bayar da takardun hukuncin da aka yanke masa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin PUNCH a ranar Talata, Lauyan dake rajin kare hakkin dan adamm Mr Femi Falana (SAN), ya ce yana kokari wajen ganin an gabatar da shari’ar.

Ya ce akwai bukatar a gabatar da komai cikin gaggawa, tunda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a makon da ya gabata yace zai sanya hannu akan hukuncin kisan da aka yankewa mawakin da zarar lokacin da aka diba masa na daukaka kara ya cika.mu kuma a jaridar legit munka samu labarin.

“Sun ki sakin takardun hukuncin da aka yanke masa, kuma lokaci na wucewa. Idan har bamu samu takardun ba baza mu iya daukaka kara ba. Kullum cewa suke takardun basu kammalu ba, kuma lokaci kara kurewa yake,” cewar Falana.

Mawakin wanda yake zaune a unguwar Sharifai a jihar Kano, an kama shi da laifin batanci ga Annabi Muhammad (SAW), a wata waka da yayi da ta dinga yawo a shafukan sadarwa a watan Maris na wannan shekarar.

Matasa dai sun kone gidansu baki daya, kuma sun gabatar da zanga-zanga ga ‘yan sanda da hukumar Hisbah akan a gabatar da hukunci akan saurayin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button