Labarai

An Rage Wa Babban Hafshin Soja mukami saboda ya fadi gaskiya Akan Yaki Da Boko Haram

Kotun Sojoji mai tuhumar jami’an ta a asirce, ta yanke wa Manjo Janar Olusegun Adeniyi hukuncin rage masa mukami, inda aka maida shi baya tsawon shekaru uku, hukuncin na nuni da cewa sai nan da shekaru uku Adeniyi zai sake kai mukamin da ya ke a yanzu.
An yanke masa hukuncin ne saboda ya fito a soshiyal midiya ya fitar da bidiyon da ake nuna shi ya na korafin rashin wadatattu da ingantattun kayan fada da sojojin Nigeria ba su da shi a fagen yaki da Boko Haram, balle har su dinga yin galaba a kan Boko Haram din
Lamarin ya faru watanni hudu da suka wuce lokacin da Janar Adeniyi ke yiwa Babban Kwamandan Operation Lafiya Dole a Jihar Yobe bayan wani artabu da Boko Haram su ka yi wa sojoji kwanton-bauna su ka kashe soja 43
Datti Assalafy ne ya wallafa a shafinsa,a cikin bidiyon, Adeniyi ya bayyana yadda sojojin su ka afka cikin tarkon kwanton-baunar da mayakan Boko Haram su ka yi musu, ya kuma yi korafin cewa akwai magulmacin da ya sanar da Boko Haram lokacin da sojojin za su wuce.
Sannan a cikin bidiyon an nuna Janar Adeniyi yana nuna hoton barnar da Boko Haram su ka yi wa sojojin, wadanda Manjo Janar Adeniyi yace Boko Haram sun zagaye su da manyan motocin yaki a kalla guda 15, bayan fitar bidiyon ne sai aka cireshi daga mukaminsa, yanzu kuma aka yanke masa hukunci
Da ake yanke masa hukuncin, an shaida masa cewa ya karya dokar soja ta watan Yuni, 2018, wadda ta haramta wa soja fitowa a fili ko a soshiyal midiya su yi korafin wata matsalar da ta dame su, wadda ya shafi tsakanin su da gwamnati ko hukumar sojojin kasar nan, a kan wannan aka rage masa mukami, tare da maida shi baya tsawon shekaru uku.
Shi kuma wani hadimin sa, wanda kurtun soja ne, an yanke masa hukuncin daurin kwanaki 28 a kurkuku tare da tilasta shi yin aikin karfi wurjanjan a lokacin da ya ke a daure, an maka masa wannan hukunci ne saboda daukar bidiyon da ya yi.
An kama Adeniyi da wannan laifin na fitowa a soshiyal midiya ya watsa bidiyon da ake ganin ya zubar da kimar rundinar sojin Nigeria, kamar yadda Premium Times ta hada rahoton
Nigeria kenan, fadin gaskiya akan yaki da Boko Haram ya zama abin laifi, sun kasa yanke wa ‘yan Boko Haram da suka kama hukunci, sun dawo suna yakar wadanda suka fadi gaskiya akan matsalar da ke faruwa a fagen yaki da Boko Haram, wannan abin tsoro ne wallahi
Allah Ka isarwa wannan hafshin soja, Allah Ka daukaka darajarshi Amin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button