Labarai

Subhanilillahi ! Boko Haram Sun Kai Sabon Mummunan Hari A Garin Magumeri A Borno (Hotuna)

Advertisment

Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kai sabon harin ta’addanci a karamar hukumar Magumeri jihar Borno, kuma sun kone Asibitin Razes, Telecoms Mast kursus.

‘Yan ta’addar sun kone wani babban asibitin cike da kayan aiki wanda Gwamnatin jihar Borno ta wadatashi da kayan aiki na zamani, sannan sun kona mota kiras tarakta wanda gwamnatin jihar Borno ta baiwa al’ummar garin domin rage wahalar manoma.

Mayakan sun mamaye garin Magumeri ne da misalin karfe 04:00 na safiyar jiya Litinin sannan suka fara harbin bindiga ba misalin karfe 04:57 na yamma wanda ya kwashe kusan 2 Duk da kokarin da sojoji suka yi na murkushe su

Amma ‘yan ta’addan sai da suka samu nasarar aiwatar da wannan ta’addanci, suka wuce abinsu suka sake kaddamar da sabon harin ta’addanci a garin Kukawa a yammaci yau Talata
Shafin Datti Assalafy ne ya ruwaito wannan labari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button