Labarai

Yan Luwadi Sun Chanza Sabon Salo A Jihar Kano

Advertisment

Ana tsakar da fuskantar matsalar ci gaba da yaduwar yima kananan Yara Luwadi musamman a jihar Kano kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wasu ‘yan daudu da kuma ke sana’ar luwadi da suke kiran mutane a waya don yin lalata da su, idan kuma ka ki amincewa sai su ce ai tabbas sun yi lalata da kai sannan sai su yi barazanar sai ka basu kudi.

‘Yan luwadin dai kamar yadda muka samu, idan har basu samu yadda suke so ba daga ga mutumin da suka kira, to sukan yi masa barazanar shiga kafafen yada labarai domin su ‘tona asirin sa’ ko kuma ta kafofin sada zumunta.

Har ila yau ana ci gaba da fuskantar barazanar kama Manyan mutane da laifin danne kananan Yara Mata a matsayin Fyade, don a makon daya gabata ma an kama wani Malamin Islamiyya, ya turmushe Dalubar sa Yar shekaru 7.

Advertisment

@JARIDAR DIMOKURADIYYA

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button