Muna Allah Wadai Da Nuna Wa Musulmi Kiyayya A Kungiyar Lauyoyin Kasa
Yanzu haka an samu adadin kungiyar Lauyoyi na jihohin Bauchi, Kaduna, Jigawa, Yobe da Kebbi wadanda suka fitar da sanarwan ficewa daga halartan taron kungiyar Lauyoyi na kasa da za’a gabatar, saboda an cire sunan Malam Nasir El-Rufai a matsayin mai gabatar da jawabi
Sannan jiya Asabar kungiyar Lauyoyi Musulmi na jihar Kaduna (MULAN) ta fitar da sanarwa ta bakin mataimakin shugaban kungiyar Barr Abbas Masanawa suka soki matakin da kungiyar lauyoyi na kasa (NBA) ta dauka akan Maigirma gwamna Malam Nasir El-Rufai, sunyi kira ga Lauyoyi Musulmai na fadin tarayyar Nigeria da su bijirewa halartan taron
Sunce abinda aka yiwa Malam Nasir El-Rufai wariya ne da kiyayya na banbancin addini wanda ba zasu lamunta ba, sannan a dayan bangare majalisar koli na addinin Musulunci ita ma ta bayyana bakin ciki akan cire sunan Malam Nasir El-Rufai da akayi saboda yana Musulmi
Kungiyar Lauyoyin Musulmi na jihar Kaduna (MULAN) sunce sunyi mamakin yadda kungiyar Lauyoyi na kasa (NBA) sukayi shiru a kan kisan da ake yiwa Musulmai a Arewa maso gabas da maso yamma, Birnin Gwari, Giwa, Kebbi, Katsina da Zamfara, amma sai gashi suna kokarin boye kisan Musulmai da wasu mabiya addini ke yi a kudancin Kaduna, don haka wannan abin takaici ne da ba za’a lamunta ba
Datti Assalafy ya kara da cewa,kundin dokar Constitution na gwamnatin Nigeria na shekarar 1999 sashi na 10 yayi dokar cewa gwamnatin tarayyar Nigeria da kowace jiha a Nigeria bata da ‘yan cin ta ayyana kanta a matsayin kasa ko jihar da take goyon bayan wani addini daya, amma a Kasarnan munga lokacin da Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya rushe Masallaci, sannan ya fito da gadara yace jihar Rivers jihar Kiristoci ne zalla, ba wanda ya isa ya tabasu, amma wani mataki kungiyar Lauyoyi na kasa ta dauka a kanshi? ba’a dauki wani mataki a kanshi ba saboda ba Musulmi bane
Jama’ar Musulmi shugaban kungiyar Lauyoyin Nigeria ba musulmi bane, sunanshi Paul Usoro (SAN) ya nuna mana cewa bai son Musulunci, abinda ya yiwa Malam Nasir El-Rufai taba kimar Musulunci da Musulmai ne
Allah Ka isar mana

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




