Martani Mai Zafi ‘Kabubali Gareku ‘Yan Dadi Arna ‘Yan Boko AQeeda ~ Daga Indabawa Aliyu Imam
‘Yan dadi arna ‘yan Boko Aqeeda/addini sun nuna damuwarsu ‘baro-baro bisa hukuncin kisa da aka yankewa wanda yayi batanci ga masoyinmu Manzon Allah S.A.W inda suke ta nuna damuwarsu kan cewa wannan hukunci bai kamata ba, suka hade kai da kiristoci suna sukan wannan hukunci.
Wadannan yara suna fakewa da musulunci suna yi wa arna aiki a fakaice, ana amfani dasu a rusa musulunci, akwai da yawa daga cikin yaran nan ‘yan dadi arna da suke mulhidai amma suke boye mulhidancinsu a zuciyarsu.
Duk kiristan da zai kalubalanci wannan hukunci tamkar yana kalubalantar littafinsu na Bible ne, domin Bible ya zo da misalin irin wannan hukunci a Leviticus 24 aya ta sha daya zuwa sama.
Ga dai yadda Bible ya zo da labarin.
11 And the Israelitish woman’s son blasphemed the name of the LORD, and cursed. And they brought him unto Moses: and his mother’s name was Shelomith, the daughter of Dibri, of the tribe of Dan:
“A yayin da d’an matar israil yayi batanci ga sunan Allah, sai aka kai shi wajen Annabi Musa A.S sunan babarsa Shelomith ‘yar Dibri kabilar Dan.”
12 And they put him in ward, that the mind of the LORD might be shewed them.
“Annabi Musa A.S ya sa aka daure shi yana jiran wahayi daga Allah kan irin hukuncin da za’a masa.”
13 And the LORD spake unto Moses, saying,
“Sai Allah yayi wahayi ga Annabi Musa A.S yana cewa dashi.”
14 Bring forth him that hath cursed without the camp; and let all that heard him lay their hands upon his head, and let all the congregation stone him.
“A fito da wanda yayi ‘batancin daga inda aka kulle shi, dukkan wadanda suka ji batancinsa su dora hannunsu a kansa, sannan jama’a su jefe shi da duwatsu.”
15 And thou shalt speak unto the children of Israel, saying, Whosoever curseth his God shall bear his sin.
“Ka kuma fada wa al’ummar isra’il cewa, duk wanda yayi batanci ga ubangiji dole ya sami hukunci.”
16 And he that blasphemeth the name of the LORD, he shall surely be put to death, and all the congregation shall certainly stone him: as well the stranger, as he that is born in the land, when he blasphemeth the name of the LORD, shall be put to death.
“Tunda har yayi ‘batanci ga sunan Allah dole a kashe shi, taron jama’a ne za’a tabbatar sun jefe shi, koda bakon cikinta, ko wanda aka haifa a cikinta in dai yayi batanci ga Allah a tabbatar an kashe shi.”
17 And he that killeth any man shall surely be put to death.
“Duk wanda ya kashe mutum a tabbatar shima an kashe shi.”
18 And he that killeth a beast shall make it good; beast for beast.
“Wanda ya kashe Dabba dole ya bayar da Dabba irinta.”
19 And if a man cause a blemish in his neighbour; as he hath done, so shall it be done to him;
“Duk wanda ya zalinci dan uwansa ayi masa irin yadda yayi.”
20 Breach for breach, eye for eye, tooth for tooth: as he hath caused a blemish in a man, so shall it be done to him again.
“Idan ya karya shi a karya shi, idan ya cire masa ido a cire masa ido, hakori da hakori, kowanne irin ciwo ne haka za’a masa.”
21 And he that killeth a beast, he shall restore it: and he that killeth a man, he shall be put to death.
“Wanda ya kashe dabba zai biya irinta, amma wanda ya kashe rai dole a kashe shi.”
22 Ye shall have one manner of law, as well for the stranger, as for one of your own country: for I am the LORD your God.
“Ya kamata ace hukunci ya zama iri guda ga d’an gari da ba’ko, tunda har nine Allah ubangijinku.”
23 And Moses spake to the children of Israel, that they should bring forth him that had cursed out of the camp, and stone him with stones. And the children of Israel did as the LORD commanded Moses.
“Sai Annabi Musa A.S yayi magana da mutanen Israel kan su fito masa da wanda yayi batanci waje don a jefe shi, suka jefe ahi kamar dai yadda Allah ya umarci Annabi Musa A.S.”
Kun ji irin hukuncin da Annabi Isah A.S ya samu al’ummar Israil na zartarwa, kuma shima a kansa ya tafi, wadannan ayoyi da muka samu a Bible Old testament suna matukar dacewa da hukuncin da musulunci yace ayi, wannan ke kara tabbatar da cewa Masoyinmu Annabi Muhammad S.A.W manzon Allah ne na gaskiya.
Ina mamakin naji kirista yana sukan wani hukunci na musulunci, bayan Bible dinsu akwai hukunce-hukunce tsaurara fiye da na musulunci.
Muna fata Allah ya shiryi wadannan yara masu cutar da addini, idan ba zasu shiryu ba Allah yayi musu abinda suka cancanta.
Indabawa Aliyu Imam





